Gwamnatin Jigawa ta maida wa Alhazan jihar kudin guzirinsu da ya yi rara a hajin Bara

0

Hukumar kula da jindadin mahajjata na jihar Jigawa JPWB ta mayar wa wasu Alhazai 2,374 da suka je aikin hajin bara kudaden da ya kai miliyan 13.36.

Kakakin hukumar Ibrahim Hashim ne ya sanar da hakan wa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Dutse ranar Laraba.

Ibrahim Hashim ya ce hukumar ta biya Alhazan kudaden sun da kudin da suka biya akan jami’an kula da rumfuna da hukumar kula da aikin haji ta kasar Saudi ta yi, da kuma wadansu kudade da Alhazan basu samu ba a wancan lokacin sannan kuma hukumar ta biya wasu maniyyata biyu da basu sami damar sauke faralin ba a wancan lokacin.

Share.

game da Author