Wani rahoto da sashen Turanci na gidan radiyon BBC ya fitar, ya bayyana yadda lauya Zannah Mustapha da ke Maiduguri ya karbo musayar daliban Chibok daga hannun kwamandojin Boko Haram.
A wata tattaunawa da aka yi da shi, lauyan ya fara da cewa, a lokacin da ya Isa wurin da zai karbo ‘yan matan su 82, bayan sun shafe shekaru uku a tsare, wani kwamanda ya rika kiran sunayen su daya bayan daya au na fitowa daga inda aka killace su domin a karbi musayar su.
Haka wadannan ‘yan mata su ka rika fitowa daya bayan daya, ana jera su daga cikin jejin kauyen Kumshe kusa da kan iyakar Nijeriya da Kamaru. Kuma dukkan su su na sanye da hijabi, jikin su a rufe tun daga fuskoki har zuwa idon-kafafu.
“Sai ni na fara zuwa wurin kafin jami’an Red Cross, aka damka min ‘yan matan.”
Zannah Mustapha dai ya dade ya na aikin shiga tsakanin sasantawa ko kokarin musayar fursunoni tsakanin gwamnatin Nijeriya da Boko Haram, musammam kokarin sako gaba dayan ‘yan matan Chibok.
A cikin shekarar 2015, Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa kafafen yada labarai cewa gwamnatin a shirye ta ce ta tattauna maslaha da ‘yan Boko Haram domin sako wadannan ‘yan mata da su ka yi garkuwa da su. Duk wani kokari da aka yi a can baya, bai yi nasara ba, domin kungiyoyin Boko Haram mabambanta sun fito sun ce da su ne za a tattauna.
Lauya Zannah Mustapha ne ya fito ya shaida wa gwamnati cewa ga kungiyar da za a tattauna da ita, kuma ita ce ke tsare da ‘yan matan. Saboda ya taba aikin shiga tsakanin da su, kuma ba su karya alkawari ba.
Ko wani zuwa da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya taba yi a Maiduguri, sai da aka saka Zannah a cikin wani kwamitin zaman sulhu.
Bayan jakadan kasar Swissland ya kai ziyara makaranta Zannah mai suna Future Prowess, a cikin 2012, sai ya shirya Wa Zannah hanyar da zai he je Birnin kasar, wato Zurich da Geneva domin a ba shi horo na musammam yadda zai zama cikakken mai shiga tsakanin bangarori biyu masu yaki da juna.
“Wancan lokaci da na karbo ‘yan mata 21, da farko 20 ne aka yi ka’idar zan karbo, amma sai su Boko Haram suka karo min wata yarinya guda daya. Suka ce sun yi min haka ne saboda yadda na ke hidima da jekala-jekala a kan al’murra da shiga tsakani da su.” Inji Zannah Mustapha.
Ya ce yadda ‘yan Boko Haram ke yi kafin su damka masu ‘yan matan, za su tambaye su daya bayan daya cewa kowace idan an taba yi mata fyade ta fadi tsakanin ta da Allah.
Haka ta fadi idan an tilasta ta auren wani ba da son ran ta ba. Akwai wata mai goyo da ta ce ita ma ba Boko Haram ne suka yi mata ciki ba, an kama ta ne a likacin da ta ke amarya, sannan angon ta ya yi mata ciki ba da dadewa ba.
Zannah ya kara da cewa wasu zaratan mambobin Boko Haram bakwai ne suka rako ‘yan matan a wurin da zai karbo muyasar su. Kuma a cikin 82 da karbo a baya-bayan nan, babu mai goyo ko guda daya.
“Ai likacin da na ce musu to a yau kun zama ‘yantattu, sai fuskokin su suka cika da wani irin murmushi mai ban tausayi. Amma ba su yi tsalle da shewar murna ba, watakila saboda su na a gaban Boko Haram din.”
“Amma a lokaci da na ce su je su shiga motoci wadanda Red Cross suka kawo domin kwashe su, kowace sai ta runtuma a guje a shiga mota kawai. Su na shiga fa sai suka fara murna da wake-waken godiya ga Allah. Wasu kuma sai kukan-dadi.”
Zannah ya ce babbar gudummawar sa a wannan aikin-sa-kai da ya ke yi, shi ne karbo wadannan ‘yan mata 82 a lokaci guda da ya yi.
Ya taba karbo kyaututtuka na yabon wannan bajinta a shekarar 2016 da 2017.
Sai dai kuma jama’a da dama na maganar makomar wasu da dama da aka tsere da su, wadanda har yanzu ake zaton su na hannun Boko Haram, kuma su ba daliban Chibok ba ne, da suka kunshi maza da mata.
Don haka ake ganin ya kamata gwamnati ta sa aniya da himma wajen ganin ta ceto su su ma.