Kasa Najeriya bata samar da na’urorin gwajin mutane cutar Ebola ba a iyakokin Najeriya musamman iyakar Seme dake jihar Legas.
Kamar yadda aka sani a makon da ya gabata ne Hukumar kiwon lafiya ta duniya ‘WHO’ ta sanar da bullowar cutar Ebola a kasar Kongo.
Ta shawarci kasashen da ke kusa da kasar ta Kongo da su samar da kariya ga mutanen su domin gudun kada ta kama yan kasashen.
Duk da haka a binciken da kamfanin dillancin labarai ta yi akan hakan ta gano cewa gwamnatin Najeriya ta samar da kayayyakin samun kariya daga cutar a tashoshin jihargen sama a dake kasan amma iyakar Seme dake jihar Legas bata sami wannan shiri ba.
Binciken ya nuna cewa har yanzu matafiya da kuma mazaunan wannan iyaka basu da labarin bullowar cutar Ebola a kasar Kongo.
Bayan haka wani ma’aikacin kiwon lafiya na wannan tashar da kuma baya son a fadi sunansa wanda ya ce gwamnati bata wadanda su da kayayyakin aiki ba wanda hakan ya ba su iya komai.
’’Mu na da labarin bullowar cutar kuma da matakan da ya kamata a samar domin hana yaduwar cutar musamman a wannan bodar domin itace ta fi yawan samun mutanen da suke fita kasan amma har yanzu babu kayan aikin da aka ba mu’’.
‘’Amma in tabbatar muku da cewa da zaran mun sami kayayyakin aikin da muke bukata za mu fara aiki.’’