Daya daga cikin shugabannin kungiyar kira a sako ‘yan matan Chibok wato ‘Free Chibok Girls’ Aisha Yesufu tayi kira ga Buhari da ya sauka daga kujeran shugabancin Najeriya tunda bashi da lafiya, idan kuma yaki ta roki majalisar kasa ta tsige shi.
Aisha ta yi wannan maganganu ne jiya a shafinta na Twitter.
Tace ” Dole ne mu dawo da martabar kasar mu Najeriya, ldan Buhari yace ba zai sauka ba, to majalisa ta tsige shi mana. Wannan kasar ba na mutum daya bane saboda haka tunda ba zai iya ba majalisa ta tsige shi kawai.
” Ace wai shugaban Kasa bashi da lafiya amma ya ki ya sauka daga kujeran shugabanci ai bai yi ma’ana ba. Bamu san wanene zai saka hannu a kasafin kudin 2017, ga sakamakon rahoton binciken Sakataren gwamnatin tarayya Babachir da akayi. Mataimakin shugaban Kasa Yemi Osinbajo yana da iyaka akan abinda zai iya yi.
” Ba za mu sa ido mu bari abubuwa na ta tabarbarewa saboda Buhari ba shi da lafiya ba. Idan ba zai sauka ba, majalisa ta tsigeshi kawai ko abubuwa zasu ci gaba a kasa Najeriya.
” Buhari Kayi shugaban Kasa sau biyu a rayuwanka, sannan ka kai matsayi janar a aikin soji duk kai kadai. Haba.
Shugaban kasa ya mika ragamar mulkin kasa ga mataimakin Yemi Osinbajo domin ci gaba da gudanar da mulki kasa Najeriya har sai ya dawo daga kasar Britaniya inda ya tafi ganin likitocin sa.