Sanatoci sun fi jami’an gwamnati tsafta idan maganar sama da fadi da kudaden gwamnati a keyi

0

An bayyana cewa bangaren ma’aikatan gwamnati sun zarce ministoci tabka wuru-wuru nesa ba kusa ba.

Wannan kalami ya fito ne daga bakin sanatoci guda biyu, Matthew Urhoghide da Bala Ibn Na’Allah, sakamakon wani kudiri da Sanata Dino Melaye ya gabatar inda ya yi zargin yin ba daidai ba a hukumar kula da kwangilan sayen kayan gwamnati.

“Mu na sane da cewa kusan kashi 70 bisa 100 na laifukan wuru-wuru duk an bankado su ne daga bangaren ma’aikatan gwamnati.

Ya kuma bayyana cewa : “Ku kalli yanayin irin harkallar da ake bankadowa, abin farin cikin shi ne, har zuwa yau duk abin da ake bankadowa din nan kashi 70 bisa 100 duk a bangaren gudanarwa na ma’aikatan gwamnati EFCC da ICPC ke bankado su.”

Shi kuwa Sanata Na-Allah, cewa ya yi ma’aikatan gwamnati ne ke kula da dukkan kwangiloli kuma su ne ke da kamfanonin da su ke ba kwangilolin. Dalili kenan yawancin kudaden ba a iya gano su.

Shi ma Sanata Urhoghibe cewa ya y ai dama ma’iakatan gwamnati maha’inta ne kwarai. Su ke ba da kwangiloli ga kan su da kan su.

Share.

game da Author