Jami’an hukumar kula da safara da fasakaurin miyagun kwayoyi na reshen jihar Gombe NDLEA sun kama wasu makiyaya biyu dauke da bindiga da wasu miyagun kwayoyi masu bugarwa.
Kwamandan hukumar Aliyu Adole ne ya sanar da hakan wa manema labarai a garin Gombe.
Aliyu yace sun yi garkuwa da Mijinyawa Shehu dan shekara 30 da bindiga kirar ”Jericho pistol” tare da shi kuma kaninsa mai suna Abdul Shehu mai shekara 25 da suke tare dauke da wasu kwayoyin da ya kai gram 300 a kauyen Wangi-Zange, karamar hukumar Dukku.
Bayan haka Adole yace ma’aikatansa sun gano harsashen bindigar boye a wajen kwanan makiyayan.
Da a ke tuhumarsa akan mallakar wannan bindiga, yace bindgan ta yi shekara biyu a hannunsa sai dai babu wani cikin ‘yan uwansa daya san cewa yana ajiye da bindigan.
Hukumar NDLEA ta ce ta danka Mijinyawa ga ‘yan sanda domin ci gaba da yin bincike akansa sannan shi kuma Abdul za su kai shi kara a babbar kotun kara domin muamula da kwayoyin da yak e yi.