Tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo ya sanarwa manema labarai cewa ya kawo wa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ziyara ta musamman ne a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kasa sannan kuma domin ya sada zumunta.
“ Kamar yadda kuka sani ne cewa tsofaffin shugabannin kasa sukan kawo wa shugaban kasa ziyara haka nima naga ya dace in kawo irin wannan ziyara wa mataimakin shugaban kasa.”
Namadi Sambo ya ziyarci Osinbajo ne yau bayan, kwanaki uku bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika ragamar mulkin kasa a hannun sa a yayin da yake ganin likitocinsa a kasar Britaniya.