Shugaban hukumar kula da rajistan motoci DRTS, Wadata Bodinga ya karyata zargin da akeyi wa jami’an hukumar na yi wa direbobin motoci a babban birnin tarayya Zamba cikin aminci duk lokacin da suka bukaci yin sabon rijista.
Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta yi bincike akan yadda irin hakan ke faruwa ga mutane cewa wai ma’aikatan na karban kudaden da bai kamala ba a wajen su iadan suke bukaci yin sabin takardun mota ko kuma canza takardun.
Wani magidanci mai suna Abraham Oyekan yace wani ma’aikacin hukumar ya yi masa zambar kudinsa har naira 12,000 da ya nemi ya canza takardun motar sa.
Yace ma’aikatar sun saba yin hakan ga masu motoci amma kuma yanzu hakan ma y aba wani jami’in hukumar kudi domin sabonta masa takardun mota tun watan Janairu amma har yanzu ba labari akai.
Shi kuwa Solomon Vongbut y ace ya bawa wani ma’aikacin tsofaffin takardun sa da kudi Naira 15,000 tun a watan Disemba domin a canza masa takardun motarsa amma har yanzu shiru kakeji kamar anci shirwa.
Ya ce idan ya kira shi a waya sai ya fada masa cewa ya yi tafiya ko kuma ya tafi aiki zuwa wani garin sannan kuma har yanzu bai karbi takardun motar tasa ba.
Shugaban hukumar DRTS Bodinga yace ma’aikatan hukumarsa basa karban kudade daga hannun direbobi saboda samarda tsafta da hukumar ta ke kokarin kawowa a hukumar kuma yace ba a taba kawo masa irin wadannan koke koke ba.
Ya gargadi direbobi da su bi ta hanyar da ya kamata domin yi ko sabonta takardun motocinsu.