Makarfi bai san kimar dan Adam ba – Lai Mohammmed

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilan da suka sa ta yi musayar wasu ‘yan Boko Haram da daliban Chibok su 82, tare kuma yin kakkausan raddi ga shugaban daya bangare na jam’iyyar PDP, Sanata Ahmed Makarfi.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ne ya ragargaji Makarfi, bayan da makarfi ya bayyana cewa gwamnati ba ta yi daidai ba, da ta mika wasu ‘yan Boko Haram aka ba ta ‘yan matan Chibok 82.

A cikin takardar da ya fitar yau Litinin a Abuja, Lai Mohammed ya ce, kalaman Sanata Makarfi “rashin mutunci ne, rashin ganin daraja da kimar dan Adam ne kuma rashin imani ne.”

Sanarwar ta Ministan Yada Labaran wadda jami’in yada labaran sa Segun Adeyemi ya sa wa hannu, ta ce rashin imani ne karara a wannan lokaci wani ya fito ya soki dalillan fito da wadannan ‘yan mata, a yayin da kasa gaba daya ake cike da taya iyayen su da iyalansu murnar kubutar da su da gwamnati ta yi.

“Amma fa ba abin mamaki ba ne don irin wannan kasassaba ta fito daga bakin dan PDP, wadanda dama sakamakon nuna rashin kula da rashin tausayin al’umma ne da suka nuna a baya ya haddasa sace ‘yan matan a lokacin da jam’iyyar su ke kan mulki.”

Lai kuma ya ce irin yadda Makarfi ya fito ya na bobbotai da borin-kunya don gwamnati ta kubutar da ‘yan matan Chibok 82, ya nuna cewa dama ita PDP tun can asali ba ta fata ko addu’ar magance kashe-kashen Boko Haram.

Ya kuma kara da cewa ba sabon abu ba ne, kuma ba daga kan Nijeriya aka fara kulla yarjejeniyar musayar fursunonin yaki ba. Lai ya ce manyan kasashen duniya kamar Amurka ta yi musayar manyan ‘yan Taliban biyar da ta ke a tsare, inda Taliban ta sako mata wani zaratan sojan ta daya mai suna Sajen Bowe Bergdahl a cikin 2014.
“Idan kuma ba a manta ba, tun a ranar da aka rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce ko an kakkabe Boko Haram, to hankalin mu ba zai kwanta ba, har sai an kubutar da ‘yan matan Chibok da suran mutane da Boko Haram suka yi garkuwa da su.”

Ba a nan Lai ya tsaya ba, ya kara da buga misalin cewa a cikin 2011 sai da Isra’ila ta saki Falasdinawa 1,027 kafin Falasdinu ta sakar mata soja guda daya tal, mai suna Gilad Shalit.

“In banda rashin kunya, kun yi sakaci an sace yara, kun zuba ido kun bar su a hannun Boko Haram, to mene ne kuma na tayar da jijiyar wuya don wannan gwamnatin ta kubutar da su ta hanyar musaya? Kun dai kara tabbatar da rashin imanin ku.” Inji Ministan Yada Labarai.

A karshe ya jaddada aniyar wannan gwamnatin wajen ganin ta kawo karshen duk wani tashin hankalin da ya addabi kasar nan. Har yanzu dai akwai sama da ‘yan mata 80 a hannun Boko Hamram, daga cikin 276 da suka sace, shekaru uku da suka gabata.

Share.

game da Author