Rikicin Kaduna: Jami’an tsaro sun cafke matasa 18

2

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun tabbatar da cewa sun kama matasa 18 da ake zargi da hannu a hatsaniyar da ta faru yau a unguarded Kabala West, Kaduna.

Hatsaniyar dai ta haifar da fada tsakanin mabiya addinin Musulunci da kuma Kiristoci.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran gwamnan jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya bayyana cewa an kafa kwamitin sasantawa tsakanin al’ummar Kabala West da ta Unguwar Mu’azu, inda Sakataren Riko na Gwamnatin Jihar Kaduna, Adullahi Ibrahim da Samuel Aruwan din ne gwamnatin ta nada, sun zauna da wakilan kungiyar Kiristoci ta CAN da Jama’atu a bangaren Musulmai na yankunan domin tattaunawar da samun zaman lafiya mai dorewa.

18402654_1514796775205980_1523318352039616274_n

Kamar yadda rahotanni ya iske mu wasu matasa ne suka tada hankalin jama’ar yankin wai domin ganin gawa a makabartar Kiristoci dake yankin. Dalilin haka sai suka far ma wasu musulmai.

Hakan bai yi wa matasan musulmai dadi ba sai suma suka far ma kiristocin unguwan.

Ko da yake duk wadannan bayanai daga bakin mazauna unguwar ne muka samo, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bata bada bayanai akan ainihin abin da ya faru ba.

Jiragen saman yaki da jami’an soji da ‘yan sanda ne suka kai dauki unguwan tun kafin abin ya wuce gona iri.

18424070_1514796778539313_3917891875142022704_n

Share.

game da Author