Jami’an ‘yan sandan Britaniya sun tuhumi dan kwallon Najeriya Ahmed Musa kan zargin lakada wa matar sa Jamila dukan tsiya a kasar da aka ce ya aikata a daren Alhamis.
Ahmed Musa dan wasan kungiyar kwallon kafan Leicester City ne.
Kamar yadda wata jaridar kasar Britaniya mai suna theSun.co.uk ta rubuto labarin yau ta ce jami’an ‘Yan sanda sun ziyarci gidan Ahmed Musa da karfe 1 na safe domin gudanar da bincike akan hakan.
Jami’an ‘yan sandan sun dauki bayanai daga bakin matar sa Jamila, mahaifiyar sa, da ‘ya’yan sa biyu, Ahmed da Halima.
Jami’an ‘yan sandan sun tabbatar da tsare Ahmed Musa saboda zargin cin mutuncin matar sa Jamila na tsawon dan wani lokaci.
Wani makwabcin Ahmed Musa a kasar ya ce bashi da masaniya akan abin da ke faruwa a cikin gidan Ahmed Musa amma dai ya san cewa Ahmed mutum ne mai hakuri.
Bayan haka dan kwallon ya rubuta sakon nuna soyayya ga matar sa a shafinsa na Instagram ya taya ta murnan zagayoar ranar haihuwar ta.