Jama’ar mazabar Kiru da Bebeji sun ce a shirye suke suyi wa dan Majalisar su Abdulmumini Jibrin Kiranye saboda maganganun da yayi akan Buhari na batanci.
Jama’ar yankin mazabun da yake wakilta sun dunguma ne zuwa ofishin jam’iyyar APC da ke jihar Kano domin mika wasikar su na neman yi masa Kiranye.
Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Kiru yace babu wanda zai hana su yi wa Abdulmumini kiranye akan irin maganganun da ya yi wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Da yake mika wasikar ga shugaban jam’iyyar na jihar Kano jogoran tafiyar yace “ Da farko dai in so in sanar muku cewa ba ma tare da Abdulmumini Jibrin akan zantuttukan da yayi kan rashin lafiyar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.”
Sarkin yakin Jibrin Abdulmumini shi ma ya nuna rashin jin dadin sa akan furucin da yayi sannan yace a gaskiya fa basa tare dashi.
“ Jibrin ya nu cewa shi ma barawo domin da kansa ya tona yadda suke satan kudin talakawa a tsawon shekarun da yayi yana majalisar wakilai.
“ Babu wani abin da yayi wa mazabun sa na azo a gani a tsawon shekarun da yayi a majalisa.
Daga karshe sun ce za su yi kungiya domin zuwa Abuja su roki shugaban kasa akan furucin da Jibrin yayi dangane da rashin lafiyar sa.