Tsohon Hafsan Hafsoshin sojojin Nijeriya, Janar Ishaya Bamaiyi, ya bayar da labari tiryan-tiryan na yadda manyan hafsoshin kasar nan suka rika tafka rikici, tuggu da tirka-tirkar wanda zai zama shugaban kasa bayan mutuwar tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, wanda ya mutu ranar 8 Ga Yuni, 1988.
Bamaiyi, wanda tsohon Laftanar Janar ne, ya bayyana wannan kwamacala ce a cikin wani littafi da ya rubuta da Turanci, mai suna “Vindication of a General” wanda aka kaddamar a ranar Alhamis da ta gabata, a Abuja.
Ya yi bayanin cewa, bayan rufe gawar Abacha a Kano, a wannan ranar sai manyan hafsoshin sojojin kasar nan suka koma Majalisar Koli a fadar Shugaban Kasa, inda suka yi taro domin a fito da wanda zai zama shugaba.
Ya ce duk da cewa shi ba shi da muradin son zama shugaban kasa, sai aka fi maida karfi wajen zaben Babban Hafsan Tsaron Kasa na lokacin, Abdulsalami Abubakar, Ministan Abuja a lokacin, Jeremiah Useni da kuma shi Bamaiyi din. Haka Bamaiyi ya bayyana a cikin shafi na 252.
“Ban taba sha’awar rike wani mukami na siyasa ba, domin na guji hakan tun tuni, kuma ba ni da niyyar zama shugaban kasa. Haka na bayyana wa manyan sojojin da ke wurin, wadanda su ka jajirce cewa ni ne zan zama shugaba a lokacin, cikin su kuwa har da Janar Victor Malu, Magashi da Patrick Aziza.”
“A lokacin ina sane da cewa wasu kananan hafsoshi wadanda ba su so na zama shugaban kasa, saboda sun san ba zan amince su ci gaba da kasancewa a cikin aikin soja ba.”
Ya kara da cewa duk da rashin sha’awar shugabanci da ya yi, matsalar da ya ke da ita dangane da Abdulsalami, ita ce an taba kama shi dumu-dumu da laifi bayan wata kotun soja da aka kafa ta binciki yadda ya yi harkallar kudaden albashin sojoji tsakanin 1970 zuwa 1972. Wannan dalilin ne ya ce ya yi tunanin da wuya idan ma ya ce a zabi Abdulsalami, wasu ba za su amince ba.
Bamaiyi ya ce “amma maimakon a daure Abdulsalami shekara biyu ko a kore shi, ko a rage masa mukami, sai ya hada kai da shugaban kwamitin binciken marigayi Kanar Nenger, wanda dama ajin su daya a Sakandaren Bida, aka sassauta masa hukunci zuwa jan-kunne.”
Bamaiyi ya kara da cewa, ana fara wancan taro a fadar Aso Rock, sai kawai Abdulsalami ya tashi ya fara raba wasu takardu, kamar ya na nufin zabe ne za mu yi kenan mu fitar da shugaban kasa.
Ya kuma ce mana, “Wani ba zai zabi duk wanda aka taba samu da aikata laifi ba a matsayin shugaban kasa. Don haka zabe za mu yi a nan mu fitar da shugaban kasa. Kenan batun wanda zai gaji Abacha ya fado kai na, kuma wasu manyan hafsoshi duk su ka ce min sai na karbi tayin zama shugaba kawai, domin na kwato kasar nan daga afkawa cikin wani mummunan hali. Ni kuma na ce musu, na amince da Abdulsalami, kawai mu goya masa baya.
“Yayin da ake cikin wannan tirka-tirka ne, wasu kananan hafsoshi sun yi ta yi min zagon kasa ni da Janar Useni. Sun yi amanna cewa muddin na zama shugaban kasa, to sun shiga uku, amma ni dama ba ni da sha’awar zama shugaban kasa ko rike wani babban mukami na siyasa.
“Yayin da na ce wa manyan hafsoshin da ke so na zama shugaba cewa ni ba na son zama, sai su ka ce min, ai kuwa sai na yi da-na-sanin rashin karbar wannan tayi da na yi. Da farko ban yarda da abin da su ka fada min ba, saboda na ga dai ni da Janar Abdulsalami shakikan abokai ne, tun daga lokacin da mu ke a matsayi Laftanar. Kuma tare mu ke yin wasan kwallon gora a Barikin Sojoji na 2 Mechanised Division, da Shehu ‘Yar’Adua da Useni.
“To mu na shiga cikin dakin taro, sai Abdulsalami ya fara raba takardu, kamar an je ne da shirin yin zabe. Dama kuma kowa daga wanda ya shiga wurin da Bebul, sai wanda ya shiga da Alkur’ani, saboda babu wanda ya san wanda za a ce shi ne za a rantsar ya zama shugaba.
Sai da aka yi ta faman shawo kan manyan hafsoshin nan domin su amince da Abdulsalami ya zama shugaban kasa,. Dalili kenan aka je da Bebul da Alkur’ani a wurin rantsuwar.”
Ya ce, “Yayin da zabe ya zo kai na, sai na mike tsaye na ce ai duk mun yarda cewa Janar Abubuakar shi ne zai zama shugaba kuma babban kwamandan askarawan kasar nan. Na kuma ce a kara masa girma zuwa Janar mai tauraro hudu, kuma ya na zaune kusa da ni. To kun ji yadda mu ka yi nasarar nada Abdilsalami shugaban kasa, duk kuwa da cewa kotu ta taba samun shi da laifin yin cuwa-cuwar kudin albashi.”
Bamaiyi ya ce ya na farin ciki cewa har yanzu takardar bayanin wannan taro ta na nan wacce wani mai suna T. Fagbemi ya rika rubuta abubuwan da suka wakana. Kuma takardar na dauke da cewa Bamaiyi din ne ya ce a nada Abdulsalami, kuma a kara masa girma zuwa Janar mai tauraro hudu.
Ya kara fada a cikin littafin nasa cewa ya yi nadamar yadda Abdulsalami ya canja bayan ya hau mulki.
Ya kara da cewa “sabon shugaban wanda ya yi mulki tsakanin 8 Ga Yuni, 1998 zuwa 29 Ga Mayu, 1999, sai ya fara kokwanton biyayya ta a gare shi, kuma ya fara yi min kallon wata barazana a gare shi.”
Dalilin da ya sa Bamaiyi ya fadi haka, shi ne, Bamaiyi bai goyi bayan yadda wasu tsoffin sojoji irin su Janar Babangida suka zartas cewa a dawo da Olusegun Obasanjo ya shugabanci Nijeriya.
“Abdulsalami ya rika yi taron sirri tsakanin sa da Janar Babangida da Janar Aliyu Gusau. Na rika samun rahoton yadda su ke haduwa wuri daya. Amma ni ban damu ba, saboda na san cewa ba wani dadewa za mu yi a gwamnati ba.
“Ashe ni ban sani ba, Janar Abdulsalami tuni shi da Babangida da TY Danjuma da Janar Aliyu Gusau duk sun amince Obasanjo ne zai dawo ya yi mulkin farar hula bayan saukar Abdulsalami. Ni kuma sai na tsaya kememe na ce ban yarda ba. Kuma haka na shaida wa gaba dayan su gaba da gaba.
To wannan matsayi da na dauka bai yi wa wadannan Janar-Janar dadi ba, sai shi kuma Janar Abubakar ya fara yin kaffa-kaffa da ni. Sai ya fara sa wasu jami’an leken asiri na sojoji su na rubuta rahotannin karya da kazafi kaina wai ni mutum ne mai cike da burin zama shugaban kasa. Domin bayan mutuwar Abacha babu wanda ya isa ya hana ni.”
Daga karshe Obasanjo ya ci zaben 1999, inda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007.