Matasa a garin Gololo da ke cikin Karamar Hukumar Gamawa ta Jihar Bauchi, sun fasa taron raba kayan tallafi da Dan Majalisar Tarayyar su ya shirya.
Dan Majalisa Honarabul Mohammed Garba Gololo ya shirya taron raba kayan ne a kauyen haihuwar sa, Gololo a ranar Lahadin da ta gabata. Baya ga fasa taron, matasan sun kutsa kai cikin sabon gidan Dan Majalisar suka yi wa kayan gidan karkaf.
An sace talabijin, bidiyo, rikoda, firji, da duk wani abin amfanin da ke cikin gidan, hatta tagogin gidan sai da aka balle. Ganau ba jiyau ba ta tabbatar wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa hatta motar da Mohammed Garba Ke ciki sai da aka fasa gilashin ta yayin da ya yi niyyar ficewa daga wurin taron, inda matasa ‘yan baberiya su ka nemi yi masa kofar-raggo su na cewa “Ba ma yi! Ba ma yi”, a lokaci guda kuma su na jifa.
Hotunan da PREMIUM TIMES HAUSA ta samu sun tabbatar da an kutsa a cikin gidan kuma an balle kofofi da tagogin gidan. Sai dai lokacin da aka shiga gidan tuni Dan Majalisar ya arce zuwa Gamawa.
Duk wani kokarin jin ta bakin sa ya ci tura, domin wayar sa a kashe ta ke. Sai dai daya daga cikin iyalan sa ya tabbatar da cewa tabbas an fasa gidan an yi sata, amma aikin barayi ne, ba daga rudanin siyasa ba ne. Wani dan garin mai suna Salisu, ya ce lokacin da abin ya faru ya na cikin garin Gololo, amma ba a daki Honarabul ba,
sai dai an fasa gilashin motar sa. Kuma a cewar sa, sharrin ‘yan adawa ne kawai.
Dan Majalisar ya fara samun rashin jituwa da mazabar sa tun bayan wata takardar koke da wasu kungiyoyin kishin matasa suka rubuta kuma su ka yada ta, wacce tun a cikin watan Yuli, 2016 PREMIUM TIMES HAUSA ta samu kwafen takardar.
Sun yi korafin cewa ba ya zuwa ganin gida kuma bai damu da kishin mazabar sa ba, sannan kuma ya je Abuja ya tare, ya na shan shagalin sa, ya bar su cikin karkara bayan sun sha wahalar zaben sa.
Bugu da kari, sun kuma nemi ya je gida ya kare kan sa daga zargin da aka yi cewa sun yi yinkurin yi wa wata Baturiya fyade a ziyarar da suka kai Amurka. Domin a cewar su bai kamata a ce ba su ji daga bakin sa ba tunda su ya ke wakilta. Sun kuma zarge shi da ba ya nuna goyon bayan sa a fili ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, alhali arzikin Buhari ya ci aka sabe shi saboda “Sak.”
Gololo ya nuna cewa ba zai je taro a garin ba, saboda ya na gudun kada a taba lafiyar jikin sa. Sai dai Premium Times ta samu bayanin cewa ya ce matasan su tura masa wakilai su zauna a Kano ko Kaduna ko kuma Abuja. Wannan tayin ne kungiyoyi irin su Majalisar Muryar Talaka da Gamawa Youth Development Forum da sauran su duk su ka ce ba su amshi goron gayyatar ba, domin a mazabar sa ya ci zabe ba a Kano ko Kaduna ko Abuja ba.
Premium Times ta samu labarin cewa Gololo ya yanke shawarar zuwa ganin gida ne bayan wani dan bautar kasa dan mazabar sa da ke aiki Abuja ya kai masa ziyara, inda ya ba shi shawara ya rika zuwa ganin-gida, kuma ya rika yin koyi da sauran abokan sa ‘yan majalisa masu nuna kishin yankin su.
Gololo ya shirya rabon kayan tallafi a Gololo da Gamawa, inda tun a ranar Lahadi da aka fara a kauyen nasa wato Gololo, ba a wanye lafiya ba.
Fitaccen dan Zabi Son Ka kuma dan asalin Gololo, Malam Malam Mai Zanen Hula Gololo, ya shaida wa Premium Times Hausa cewa abin ya yi muni kwarai, domin an yi wa gidan kaca-kaca, hatta sili da tagogi sai da aka balle. Sai dai ya ce “ita siyasa idan mutum bai dauko kudi ya na ba mutane, to sai su tsane shi.”
Da aka tambaye shi ko wakilin na su ya na zuwa ganin-gida a kai a kai, sai ya ce ya ce “ya kan zo, amma ko ya zo ba na sani tunda ni ba zuwa nake wurin sa idan ma ya zo ba. Kuma akwai kwalbatoci da ya aka yi mana.”
“Wallahi idan ka ga yadda aka yi wa gidan sa kaca-kaca, kai ka ce yaki ne aka yi mahara suka dira gidan.” Hatta kyauren gidan fa Gololo ya ce dai da wani ya je da diga, har ya fara gaggabe shi, sai sojoji suka kore shi.
Adamu wanda aka yi yamutsin a gaban sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa tun a wurin rabon kekunan dinki aka fara rikici. “Matasa sun nemi su daka wawaso ganin cewa kekunan dinkin ba su kai yawan da kowa zai samu ba, dama guda uku aka tsara ba kowace mazaba.”
Kamar yadda ya bayyana, “bayan jami’an tsaro sun hana, dai aka bada shawarar ko dai a he ofishin ‘yan sanda ko Gamawa a raba kayan. Bayan an zuba a mota ne fa aka tayar da rudani, Allah ya sa akwai jami’an tsaro.”
Aminu ya ce bayan Dan Majalisa sun fice da kyar zuwa Gamawa, sai matasa suka darkaki gidan sa suka babballe gidan.
Ya ce tilas ya gudu don kada a je kame a hada da shi.
Sai dai ya tabbatar da cewa rabon da wakilin na su ya je ganin-gida, tun ranar Sallah Babba, a ranar ma bai yi sallama da kowa ba, ya sulale ya bar garin.
A zuwa yanzu dai an kama mutane hudu an tasa keyar su zuwa babban ofishin ‘yan sanda na Bauchi.