Wa ZeeZee tafi Aji? Ba za tayi tasiri a Fim yanzu ba – Umma Shehu

0

Shahararriyar ‘Yar wasan fina-finan Hausa Umma Shehu ta mai wa Ummi ZeeZee martini kan cewa da tayi wai har yanzu ta fi duk wata ‘yar wasan Hausa Aji.

Ta ce ZeeZee ba ta isa ta hada kanta da jaruman da suke fim ba yanzu. Ta kara da cewa ko ada din ma ZeeZee ba wata aba bace a harkar fim domin bata kai matsayin jarumai irin su Fati Mohammed ba, Safiya Musa da su Mansurah Isah ba.

Ta ce Jarumai kamarsu Jameela Nagudu, Nafeesat Abdullahi, Aisha Tsamiya, Hadiza gabon sun yi mata zarra kuma ko yanzu ta dawo babu wata rawar da zata iya takawa da zai zarce su da suke farfajiyar a yanzu.

Ga hirar da gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta yi da Jaruma Umma Shehu a Abuja.

PT: Menene zaki ce akan furicin da ZeeZee ta yi wai tafi ku aji har yanzu?

UMMA: Wannan ra’ayi n tane amma ni na sani cewa ko a zamanin da take fim, it aba sa’an su Fati Mohammed, ko Safiya Musa da dai sauransu bane. Ta dai yi iya abin da zata iya ballan tana yanzu da akwai gwanaye da yawa.

Tana dai neman a waiwaye ta ne kawai amma ba wai hakan bane. Amma jaruman yanzu ai ba sa’o’in ta bane. Ko dawowa tayi yanzu babu tasirin da zatayi a harkar fim domin an riga an wuce sanin ta.

PT: Ba kya ganin ko don tana ganin baku kware bane har yanzu ko kuma ba kwa birgeta?

UMMA: ZeeZee dai ta fadi abinda ta ke so ta fadi amma kowa yasan ba haka bane. Kamar yadda na gaya maka. An riga anyi mata zarra yanzu kuma ko ta dawo sai dai tayi kallo amma bawai ta yi wani abinda jaruman yanzu ba sayi ba.

PT: A ganinki menene ya sa ta fadi hakan to?

UMMA: An san ZeeZee da yin yawo a gari da motaci irin na kasaita dauke da sunanta. Hakan ya sa tana ganin ita gwana ce. Ni ban san inda ta sami kudinta ba da wadannan motoci amma yanzu ina suke. Ta sani wadanna tarin motoci ba su bane jarumtaka kuma bashi da nasaba da wai dalilin kwarewarta ne ta sami wannan daukaka. Ba zance komai akan arzikinta ba domin bai shafeni ba amma maganar harkar fim lokacin ta ya wuce sai dai tayi hakuri. Amma idan ta na ganin zata Iya to, ga fili ga doki.

PT: Anya ba kishi ko ku keyi da ita ba don ta fi ku?

UMMA: A’a bana kishinta domin na kalli fina-finan da ta yi kuma ban ga wani abin burgewa da tayi da zai sa wai har ince zan yi kishi da ita ba musamman idan har zaka kwatantashi da yadda ake feke biri har wutsiya a harkar yanzu. Ni bana kishinta.

PT: Kina ganin zaki iya ja da ZeeZee idan ta dawo harkar fim?

UMMA: Kwarai da gaske. A zamaninta ta yi iya abinda ta yi amma yanzu ruwa bat saran Kwando domin jaruman yanzu sun wuce sanin ta. Amma idan taga zata iya ta dawo a fafata da matan fim din na yanzu.

PT: Kina ganin kema kin kai matsayin a kiraki fitacciyar yar Fim a wannan Zamanin?

UMMA: A’a, Ni ma ina koya daga jarumai kamarsu Jamila Nagudu, Nafeesat Abdullahi, Hadiza Gabon, Aisha Tsamiya, Fati Washa da dai sauransu. Amma fa ni ma goga ce a iya nawa matsayin kuma indai ZeeZee ce ban ga alamar za ta iya ja da mu ba.

PT: Kina kwaunarta?

UMMA: Kwarai da gaske ina kaunarta sosai domin tayi sana’ar da nake ciki.

Share.

game da Author