Masu cewa Buhari ya sauka, suna fadin ra’ayinsu ne, ‘Yan Najeriya na ci gaba da yi masa Addu’a – Femi Adesina

0

Mai ba shugaban kasa Shawara akan harkan yada labarai, Femi Adesina ya ce duk wadanda suke kira Buhari ya sauka daga kujeran shugabancin kasa Najeriya saboda rashin lafiyar da yake fama dashi suna fadin ra’ayinsu ne.

Shugaban Kasa ya tafi kasar Ingila a wanacan lokacin domin ganin likitocinsa kuma ‘Yan Najeriya sun yi ta binsa da addu’a Allah ya dawo dashi lafiya , haka ma yanzu za’a ci gaba da addu’o’I Allah ya bashi Lafiya.

Buhari bai sami daman fitowa Sallar Juma’a ba yau, bayan makonni biyu Kenan bai shugabanci kwamitin Zartaswa ba.

Share.

game da Author