Jagorara tafiyar kuma ma’ajin Jam’iyyar APC, Nasiru Usman ne ya mika dukkansu ga jam’iyyar a Karamar hukmar kankiya dake jihar Katsina.
Yace dukkan su sun amince su fice daga jam’iyyar APC din ne saboda watsi dasu da jam’iyyar tayi.
“ Sanin kowa ne cewa na jagoranci mutane domin yi wa APC kamfen har ta samu nasara a zaben 2015.
“ Na yi kamfen a wannan lokacin wanda hakan ya sa tsohon shugaban karamar hukumar ya fadi zabe.
Yace jam’iyyar APC ta ki dawo da shi jam’iyyar bayan uwar jam’iyyar na shiyar Arewa maso Yamma ta ce a dawo da shi.
Nasiru yace ba ya canza sheka bane domin ya yi takara, sun gaji ne kawai da irin halin ko in kula ne da jam’iyyar APC ta keyi musu a jihar.