Cocin COCIN ta gudanar da taron musanyan ra’ayi da tunatarwa ga kiristoci Fulani da suke fadin Kasa Najeriya.
Sama da Fulani kiristoci 400 ne da suka halarci taron akayi kira a garesu da su mai da hankali wajen kira ga jin tsoron Allah da bin karantarwan Yesu Almasihu.
Shugaban cocin COCIN Copper Sebok wanda shine ya jagoranci taron ya ba da tsokaci akan makasidin shirya taron in da ya ce an shirya wannan taro ne domin a jawo hankalin Kiristoci Fulani duka akan mahimmancin hadin kai da zaman a tsakanin su da mutanen kasa baki daya.
Da yake jawabi a madadin kiristoci Fulani, Rabaren Hassan Mohammed wanda yana daya daga cikin Rabarori Bakwai da Fulani ke da su ya ce ya nagode wa Allah da ya nuna musu sabowar hanya wato addinin kirista sannan ya kara da cewa wannan taro ya dada wayar musu da kai kan yadda zasu fantsama wajen wa’azantar da ‘yan uwan su Fulani da sauran mutane addinin kirista.