Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tsare Sule Lamido

0

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido na nan a tsare a ofishin ‘yan sanda a jihar Kano.

Sule ne ya kai kansa ofishin ‘yan sanda bayan sun nemi da yabayyana a ofishin Yau lahadi.

A na tuhumar Sule Lamido ne da laifin ingiza magoya bayan sa idan har jam’iyyar sa ta PDP bata sami nasara ba a zaben kananan hukumomi da za’a yi a jihar a watan Yuli.

An tura jami’an ‘yan sanda da su je gidajensa na Kano da Jigawa domin gudanar da bincike.

Share.

game da Author