Tun bayan kiran da gwamnan jihar Bauchi yayi ga sarakuna da mutanen jihar da su dukufa wajen yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’o’I, matan aure suma ba’a barsu a baya ba a jihar.
Kamar yadda Ahmadu Bauchi ya sanar mana, mata sukan taru a gidajensu domin gudanar da irin wadannan addu’o’I ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.