Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da kafa wata sabuwar doka da zai hana ko wani irin taro ko zama da ya wuce mutum biyu a fadin jihar.
Gwamna Masari yace duk taron da ya wuce na mutum biyu yanzu laifi ne a jihar Katsina.
Sanarwan ta kara da cewa dokar ta hada da duk wanda aka kama dauke da makami, ko wani abu da zai iya ji wa mutum ciwo ko kuma yayi sanadiyyar mutuwarsa.
Mutanen jihar Katsina da su ka tattauna da PREMIUM TIMES akan wanna sabuwar doka sun ce iri wannan doka bai dace ba.
“ Mun yi matukar mamakin kafa irin wannan doka duk da mun sani ya na da nasaba da samamen da jami’an tsaro suka kai wa ‘yan kungiyar Shi’a a garin.” Inji Saidu Katsina.