Ban san ainihin shekaru na ba – Inji Obasanjo

0

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo yace bai zai iya fadin ainihin shekarunsa ba, yace yana dai amfani da shekarun sa’o’insa ne domin kintata shekarunsa.

Yace iyayensa ba masu ilimi bane a wancan lokacin saboda haka basu da masaniya akan ainihin ranar da aka haifeshi.
“Tun da nake karami na nemi iyayena su gaya mini ranar haihuwa na amma kullum na tambaya sai su ce mini basu sani ba.

Mahaifiyata takan ce mini wai ta haifeni ranar kasuwan garin mu ne amma babu wata takamammiyar rana da zata ce wai shi ne aka haifeni.

Na gaji da amsa tambayoyi da ga abokanaina a lokacin da nake karami a kauyen mu.

Obasanjo ya bada tarihin sa ne a taron kaddamar da wata littafi da ya rubuta domin yara a babban dakin karatunsa dake garin Abeokuta.

Share.

game da Author