Babbar kotu dake garin Abuja, ta bayar da belin tsohon shugaban kamfanin man na kasa (NNPC) Andrew Yakubu.
Kotun ta bayar da belinsa ne a kan naira miliyan 300, sannan ya kuma gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa.
A watan Faburairu ne hukumar EFCC, ta kama Andrew Yakubu sakamakon bankado wasu akwatuna cike da miliyoyin daloli a wani gidansa dake Unguwan Sabon Tasah dake Kaduna.