Albarkar noma da aka samu bara ya farfado da tattalin arzikin kasa Najeriya – Inji Garba Shehu

0

Kakakin shugaban kasa Garba Shehu yace kasa Najeriya ta fara farfadowa daga matsalolin da ta shiga a dalilin koma bayan tattalin arzikin kasa da ta fada saboda irin kyawawan sakamakon da ke fitowa a musamman fanin ayyukan noma.

Ya ce an samu nasarar hakan ne saboda kokarin da gwanmati ta yi wajen bunkasa aiyukan noma musamman noman shinkafa da kuma rufe boda da ta yi.

“A shekarar 2014 Najeriya ta shigo da tan miliyan 1.2 na shinkafa amma a shekarar 2015 tan tan 58,000 kawai aka shiga da shi. “

Garba Shehu ya ce mafi yawan-yawan kamfanonin dake sarrafa shinkafar bature dake kasashen waje kamar kasar Thailand sun daina aiki saboda Najeriya ta daina siyan shinkafar su.

Ya kuma ce gwamnati na goyan bayan kokarin da ma’aikatar noma ke yi na bunkasa harkar noma a sauran jihohin kasa Najeriya.

Garba Shehu yace gwamnati za ta tallafa wa kamfanonin da ke sarrafa shikafa kamar su kamfanonin BUA dake jihar Jigawa, Dangote dake jihar Kano, OLAM dake jihar Nasarawa, WACOTT dake jihar Kebbi, da kungiyar wasu ‘yan kasuwar da tsohon gwamnan jihar Anambra ya ke shugabanta.

Ya ce yanzu haka kudin buhun taki ya sauka zuwa 5,500 daga 9,000.

Daga karshe ya ce kasa Najeriya na da kamfanonin yin taki da ya kai 32 wanda sukayi shekaru da dama basu aiki amma yanzu rabi daga cikin su sun fara aiki kuma ta dalilin haka mutane da dama musamman matasa sun sami aikin yi.

Share.

game da Author