Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya, Kwamared Shehu Sani yace babu wani gwamna a kasar nan da yake da hurumin yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari fada akan yadda yake gudanar da mulki.
Shehu Sani ya fadi hakanne a karamar hukumar Chikun lokacin da yake ganawa da shugabannin karamar hukumar.
Sanata Sani yace Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi aikin da wasu da yawa daga cikin gwamnonin kasar nan basuyi ba bayan kuma ya na kokarin ganin cewa a duk lokacin da suke bukatar kudi ya na amincewa da abasu.
“Kuna karban kason kudaden jihohin ku da na Kananan hukumomi duk wata sabo da haka banga dalilin da za’a ce wai Buhari ne ya gaza ba.
“Idan ba kwa son Buhari ya rike ko kuma ya kusanci aminansa toh kuma sai ku tarwatsa naku aminan dake zagaye da ku.
“Shehu Sani ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da kada ya daga hannun kowa a zaben 2019 ya bari kowa halinsa ta ficceshi.