Majalisar Dattijai ta ki zama domin tantance kwamishinonin zabe saboda kin cire Magu

0

Majalisar ta ce ba za ta tantance kwamishinonin zaben ba idan ba har zai Buhari ya tsige Ibrahim Magu daga kujeran shugaban cin Hukumar EFCC da yake yi a yanzu.

Majalisar ta amince da wannan matsayar ne bayan tattaunawar sirri da sukayi a zauren Majalisar.

Sau biyu ne dai fadar shugaban Kasa na tura sunan Ibrahim Magu domin samun amincewar majalisar dattijai domin zama shugaban hukumar EFCC din amma hakan ya gagara.

Mai ba shugaban Kasa shawara akan harkar majalisar dattijai sanata Ita Enang yace fadar shugaban kasar zata duba wannan tirjewa da majalisar dattijai din tayi akan zaman Ibrahim Magu domin samun mafita mai dorewa.

Ita Enang yace Majalisar dattijai ba majalisa bace wanda za’ayi wasa da ita.

Share.

game da Author