Mayakan Boko Haram sun yi garkuwa da wadansu matasa 10 a jihar Barno

0

Kwamandan rundunar jami’an tsaron farar hula, NSCDC na jihar Borno Ibrahim Abdullahi yace Boko Haram ta kai wa wasu kauyukan karamar hukumar Konduga hari inda suka yi garkuwa da mata 4 da matasa maza 6 a ranar Talata din nan.

Kauyukan sun hada da Mittiri, Akalli da Arribbari.

Bayan haka kuma kwamandan ya ce jami’ansa sun gano maboyar ‘yan Boko Haram a wata kauye mai suna Dalla Fatimiri inda suke fitowa yin garkuwa da mutane a kan Babura.

Ya ce kungiyar na yin garkuwa ne da mutane musamman matasa maza domin su sami mayakan da za su iya amfani da su wajen cin ma burin su bayan ci gaba da dakile su da sojin Najeriya ta ta keyi a jihar Barno.

Bayan haka kwamandan ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman wadanda suke sansanonin ‘yan gudun hijira da su sa idanuwa sosai akan wadanda basu gane su ba a sansanoninsu sannan su sanar da jami’an tsaro hakan kuma su nisanta da zuwa inda suka sani babu cikakken tsaro a wajen.

Share.

game da Author