Darektan kamfen ɗin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya hori masu zaɓe da su bi ra’ayinsu a lokacin jefa ƙuri’a.
Lalong ya karyata raɗeraɗin da ake ta yadawa wai Paparoma bai amince da mukamin shugaban Kamfen din Tinubu ba.
” Ni da kuke gani babban mabiyin cocin Katolika kuma cikakken domin har mukami ina da shi. Paparoma bai ce komai ba game da mukamin shugabancin darektan kamfen ɗin Tinubu ba.
” Wasu ne suke ta neman kago abinda bashi da karfin tsiya don su kawo ruɗani. A matsayina na jigo a jam’iyyar APC sannan shugaban kungiyar gwamnonin Arewa. Wannan siyasa ne ɗan da haka babu abinda ya hada addini da shi.
” Babu tilas a wannan harka, idan lokacin zaɓe yayi, kana da damar ka zaɓi wanda kake so, musulmine ko kirista, babu tilas. Amma adaina kawo ruɗani a cikin abin.
Lalon ya kara da cewa shi gwamna ne na kowa da kowa, musulmi ne kai ko kirista, kai ko ma wanda bashi da addini, doka ta ce kowa ya mulke shi da adalci.
” Wasu ne da suka runanin za a nadasu mataimakin shugaban kasa suke ruruta abin da ba haka ba. Suna kokarin sakala sunana a ciki kwamacalar su. Hanyar jirgi da ban na mota da ban.
Discussion about this post