Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta kama wata tsohuwa mai suna Nsa Heneswa da ake zargi da yin garkuwa da yara Almajirai uku sannan da hannu wajen yin safarar mutane zuwa wasu wurare.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdu Umar wanda ya sanar da haka wa manema labarai a garin Maiduguri ya ce ‘yan sandan sun kama tsohuwar a tashar mota na Borno express ranar 4 ga Agusta.
Umar ya ce da tsohuwar ta iso Maiduguri sai ta shiga kasuwar dake ci ranar litini inda ta ga yara almajirai uku na bara a bakin titi daga nan sai ta sace su.
“Da farko tsohuwar ta tafi da Almajiri daya ne inda ta bashi naira 200 sannan ta ce ya zo suje ta siya masa kayan sakawa sadaka.
“Tsohuwar ta kuma je wurin ‘yan nono dake Bulumkutu inda ta sace dan wata mata dake siyar da nono mai suna Amina Ayuba.
Ya ce da ta iso tashar motocin sai ta nemi motar zuwa jihar Legas inda ‘yan union suka ce mata motan ta tashi.
“Daga nan sai ta roki a bata wuri ta kwana, washe gari sai ta fita ta sato yaro na uku.
“Sai dai dubunta ya cika ne a lokacin da ta yi kokarin sace ɗan wata mata mai siyar da abinci a tashar.
Wani direba da bai amince da yadda take ta safara a a tashar motar ba ya
Umar ya ce an kama matar Kuma an damkata ga ‘yan sanda.
Ya ce da take hannun ‘yan sanda Heneswa ta tabbatar cewa tana shirin kai yaran jihar Legas ne.
Umar ya ce ga dukan alamu Heneswa da abokan aikinta na safaran mutanen ne.
Discussion about this post