Idan ba a manta ba a wani abin tashin hankali da ban tsoro da ya auku a hanyar Ibi zuwa Jalingo, dake jihar Taraba ranar Laraba shine yadda gungun sojoji suka yi wa tawagar ‘yan sandan kwantar bauna suka kashe ‘yan sanda uku.
Kakakin rundunar ‘Yan sanda Frank Mba ya bayyana haka a takarda da ya fitar ranar Laraba cewa sojojin sun budewa ‘yan sandan wuta ne bayan sun kamo wani gogarman masu garkuwa da aka dade ana farautar sa mai suna Alhaji Hamisu.
Frank yace Hamisu yayi kaurin suna a wannan yanki wajen yin garkuwa da mutane.
‘Yan sandan sun farwa maboyar sa ne inda suka kamo shi zasu kai shi garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.
” Jami’an ‘yan sandan sun isa shingen sojojin ne inda da ganin su sai suka bude musu wuta duk da sun gane cewa ‘Yan sanda ne ke tahowa. Bayan sun kashe uku daga ciki sai suka saki Alhaji Hamisu a wannan daji.
Sai dai kuma Kakakin rundunar Sojojin Najeriya, Sagir Musa ya bayyana cewa ba da gangar bane sojojin suka budewa yan sanda wuta ba.
” Abinda ya faru shine, Sojoji sun bi wannan mota da ke dauke da wasu masu garkuwa da mutane bayan wasu kauyawa sun yi waya cewa wasu sun yi garkuwa da Alhaji Hamisu, gogarman masu garkuwa a wannan yanki. Sau uku sojoji na kokarin tsayar da wannan mota kirar Bas fara amma suna kin tsayawa.
” Bayan haka ne sojoji suka bi motar a baya suka bude mata wuta. Sai bayan motar ta tsaya ne sannan suka gane cewa akwai ‘yan sanda a ciki.
Sagir yace an kashe masu garkuwa 4 sannan wasu sun samu rauni a jikin su.
Discussion about this post