BELIN EL-ZAKZAKY: Gwamnatin Kaduna ta kakaba masa tsauraran sharuddan fita neman magani

0

Gwamnatin Jihar Kaduna ta garzaya Babbar Kotun Jihar Kaduna inda ta shigar da wasu tsauraran sharuddan yadda za a sa-ido a kan tafiyar da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky zai yi, zuwa Indiya domin neman magani.

Malamin zai yi tafiyar ne tare da maidakin sa, Zeenah, kamar yadda kotun Kaduna ta amince masa.

Kotun ta amince ya fita kasar Indiya neman magani, bayan da lauyoyin sa suka gamsar da kotun cewa tabbas shi da matar sa sun a bukatar kulawar gaggawa, bayann sun shafe kusana shekaru hudu a tsare.

Gwamnatin jihar Kaduna, wacce tun da farko ba ta goyi bayan a bai wa malamin damar fita waje neman magani ba, a yanzu kuma ta nemi kotun ta kakaba masa wadannan sharudda kafin a bar shi ya fice daga kasar nan.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Al’amurran Tsaron Cikin Gida ne ya fitar da sanarwar, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.

Duk da Kwamitin Bincike ya ce a hukunta wasu sojoji a bisa rawar da suka taka, har yau ba a hukunta ko daya daga cikin su ba, amma kuma sai El-zakzaky aka gurfanar a kotun Kaduna, bayan gwamnatin tarayya ta tsare shi tsawon lokaci ba ta tare da gurfanar da shi ba.

Jami’an DSS sun bayyana cewa za su bi umarnin da kotu ta bayar na sakin malamin ya tafi neman magani. Sai dai kuma har zuwa ranar Laraba ba ta sake shi ba.

Kwatsam, sai kuma ga bukatar da Gwamnatin Kaduna ta shigar a jiya Laraba din, wadanda ta ke neman a kakaba wa El-Zakzaky kafin a ba shi damar tafiya Indiya neman magani.

EL-ZAKZAKY: RIJIYA TA BADA RUWA, GUGA NA NEMAN HANAWA

Sharudda 7 Da Gwamnatin Kaduna TA Nemi Kotu Ta Kakaba Wa El-Zakzaky:

1. Sai Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ga hujja daga Asibitin Medanta na Indiya, cewa lallai can din ne za a duba lafiyar su El-Zakzaky, kuma sai an tsara sharuddan amincewar su cewa da sharuddan tafiya neman magani a bisa tasarin diflomasiyya.

2. Masu tafiya neman maganin a tabbatar sun sa hannun amincewa cewa idan sun warke za su dawo Najeriya su ci gaba da fuskantar shari’ar da suke yi. Sannan kuma su da kan su ne za su dauki nauyin kudin tafiyar su da na dawowar su, kudin yi musu magani da kudin hidindimun zaman su a Indiya a tsawon lokacin da za su yi a can.

3. Dole su kawo masu belin da za su tsaya musu, mutum biyu wadanda za su iya gabatar da su a duk lokacin da aka neme su. Daya daga cikin masu belin ya kasance basarake ne mai daraja ta daya dan jihar Kaduna. Daya kuma ya kasance sananne ne a jihar Kaduna. Dukkan su biyu din su kasance su na da gida a cikin Jihar Kaduna.

4. Gwamnatin Najeriya ta samu tabbataci a rubuce daga Gwamnatin Indiya cewa idan su El-zakzaky sun nemi a ba su mafaka, to ba za ta bas u ba. Sannan kuma ta haramta musu gudanar da duk wasu aikace-aikacen da abin da ya kais u kasar ne su yi ba. Musamman abin da zai zama barazana ga Najeriya.

5. Su rubuta takardar amincewa ta hannun lauyoyin su cewa idan sun je Indiya ba za su yi wasu abubuwan da za su zama barazana ko cutarwa ga ci gaba da shari’ar su da ake yi ba, ko barazana ga tsaron kasar nan da kasar Indiya.

6. Jami’an tsaro daga Najeriya su raka su zuwa Indiya neman magani, kuma su kasance tare da su a iya tsawon lokacin da za su kasance a Indiya, har dawowar su Najeriya.

7. Sai Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Indiya ya amince kuma ya tantance duk wani wanda zai kai musu ziyara a asibiti tukunna kafin a bari ya gana da su.

Share.

game da Author