Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato Tyopev Terna ya bayyana cewa mutane biyar sun rasu a hari da wasu ‘yan bindiga suka akai kauyen Rawuru, dake karamar hukumar Barikin Ladi dake jihar.
Su dai wadannan mutane sun gamu da ajalin su ne a hanyar su ta dawowa daga wani kauye dake kusa da su bayan sun halarci bukin zagayowar ranar haihuwar wani abokin su.
Adaidai suna dawowa Rawuru da misalin karfe 9 na dare sai wasu dauke da bindigogi suka far musu inda a nan take suka kashe mutane 5 sannan biyu daga cikin su suka sami rauni.
Tyopev Terna ya ce tuni har a kai wadannan mutane asibiti sannan an karo yawan jami’an tsaro wannan yanki domin samar da tsaro kamar yadda ya kamata.
Discussion about this post