Wani abu da zaka ji mata na yawan fadi musamman matan aure a Arewacin Najeriya tun ba yanzu ba shine maganan gyaran jikin mace.
Idan mace za ta yi aure za ka ga iyaye na ta kokarin a gyara ta saboda mijinta ya ji dadin ta a matsayin matar sa musamman idan ya kai ga za a sadu a yi jima’i.
Bayan haka zaka ga ana dan binsu da wasu dan ganyayyaki, hayaki ne da shayin sha duk don a gyara wuri kamar yadda ake fadi.
Shi wannan sinadarin gyara wuri kamar yadda a ke fadin an yi masa suna da ‘KAYAN MATA’. Shi dai wannan Kayan mata ya samo asali ne daga Arewacin Najeriya. Sai dai kuma yanzu wannan lakani ya zarce Arewa har ‘Kudu ma sun lakance yin amfani shi wajen gyara jikin su domin samun jima’i mai armashi da kuma karkato da hankalin namiji zuwa gare su.
Wakiliyar PREMIUM TIMES, Nike Adebowale ta yi kicibus da irin wannan lakani a kasuwar Wuse dake Abuja inda ta fada wani shago da ake wannan harka na siyar da ‘Kayan Mata’.
A wannan shago da ba ma Bahaushe bane ke kasuwancin Kayan Matan ta tattauna da shi sannan ya ce mata ya kwana biyu yana yin wannan sana’a.
” Mata kan zo nan su nemi maganin da zai dan rage musu fadin gaban su sannan ya sa su yi dadi a wajen saduwa da namiji. Anan mukan basu wanda zasu sha da zuma wasu kuma kamar shayi ne zasu sha wasu hayaki ne. Kuma suna jin dadin sa. Mukan siyar da wannan hadi har naira 25,000 zuwa 50,000 ma.
Wata budurwa yar shekara 20 mai suna Amaka, ta ce tuni ita tayi nisa a amfani da kayan mata domin ba karamin alkhairi ta ke samu da wannan abu ba a wajen maza.
” Duk abin da nake so ina samu. Ina da motan hawa, ina da shagon gyaran kai sannan an kama mini gida mai daki uku a Abuja duk sabo da yadda ake jin dadi na a gado. Da farko dai na dan ji tsoro da aka nuna mini harkar amma yanzu nine nike koya wa wasu, tabarkallah.
Mata da dama da Nike ta tattauna da su sun bayyana mata cewa Kayan Mata shine mafita ga duk wata mace idan dai tana so maza su rika muradin ta suna yi mata bita zai-zai.
Hawwa ta gargadi mutane da ke ganin wai wani asiri ne wannan abu da ake kira ‘Kayan Mata. ” Ba asiri bane gyara jiki ne kawai.” Tace akwai kawayenta da dama da suka fice daga gidajen auren su saboda matsalar harkar saduwa da mazajen su. ” Na yi ta basu shawarar yin wannan abu amma suka ki. Wasunsu da suka gano bakin zaren tuni sun saurari huduba ta sun gyara kan su. Sukan dawo su ce mini yanzu fa maigida har yaren Faransa yake yi idan harka tayi harka.
Ita ko Grace cewa tayi a dalilin harka da kayan mata ta samu duk irin abin da take burin mallaka a wurin namiji. ” Na gyara kai na zan-zan nike kuma ina samun abin da nake so.
Likiotocin da muka zanta da su ba fadi wani aibi ga yin amafani da wadannan abubuwa ba ga ‘ya mace.