Tsakanin EL-RUFAI da FASTO ENENCHE: Muna tare da Fasto Enenche na Cocin Dunamis – Inji Kungiyar CAN

0

Kungiya Kiristocin Najeriya ta bayyana cewa kungiyar na tare da Fasto Enence na Cocin Dunamis bisa korafin da yayi cewa gwamnan Kadna na sane da kisan Sarkin Adara da aka yi a watannin da suka gabata.

Idan ba a manta ba Fasto Enenche ya yi kowar cewa wai da hadin bakin gwamna El-Rufai a kashe sarkin na Adara.

Sai dai kuma bayan haka gwamna El-Rufai ya fito karara inda ya fadi wa duniya cewa bashi da masaniya game da kisan da aka yi wa wannan basaraken.

Haka kuma mataimakin sa Barnabas Bantex wanda Kirista ne kuma dan yankin kudancin Kaduna ya yi irin wannan shela inda ya ke kare gwamnan sa daga irin wannan zargi.

“Maganar gaskiya, mu na cike da mamakin yadda wasu fasto-fasto ke ta yada kalamai na kiyayya tare da da ruruta wutar fitina da kokarin harzuka mutane sake tayar da zaune tsaye, wanda hakan zai iya sake haifar da barkewar mummunan rikici.

“To ba fa za mu aminta da masu rura wutar fitina a cikin al’umma ba, ko da kuwa addinin mu daya da su.

“Mun yi mamakin yadda wasu shugabannin coci-coci suka wofintar da imanin su ta hanyar watsa kalamai na fitina da rura wutar mummunan rikici a Jihar Kaduna. Abin takaici ne kwarai da bacin rai irin yadda muka ganin wasu faya-fayan bidiyon da aka rika yadawa, inda wadannan masu kiran kan su fasto ke ta tunzura mabiyan su.

“Baya ga tunzura mabiyan su da cewa wai dokar hana fita a yankin da kiristoci suke zaune kadai ta shafa don a kuntata musu, fastocin sun kuma wuce-gona-da-iri, ta hanyar kantara wa gwamnatin jiha karyar cewa ta na da hannu wajen kisan Agom na Adara, Maiwada Galadima. Don haka kalaman da suke furtawa na dalilin kisan basaraken, abin dubawa ne ga jami’an tsaro.

“A matsayin mu na manyan kiristoci da ke cikin wannan gwamnati, mu na karyata wadannan karairayin na su da cewa:

“A ranar da aka yi garkuwa da Agom na Adara, ba daga wurin halartar taro tare da Gwamna ko wani jami’in gwamnati ya ke ba.” Kamar yadda Bantex ya fadi.

Sai dai gwamna El-Rufai ya yi ikirarin maka Enenche a kotu domin acewar sa yayi masa Kazafi ne cewa wai yana da hannu a kisar da aka yi wa Sarkin Adara din.

Hakan bai yi wa kungiyar Kiristoci dadi inda suka gargadi gwamna El-Erufai da ya shiga taitayin sa bisa ga abin da yake kitsawa gawannan fasto.

A doguwar sanarwa da suka fitar, kungiyar CAN ta ce tana tare da Fasto Enenche 100 bisa 100 cewa magangaun da yayi bai kece doka ba domin ya fadi ta ne kamar yadda ya ji shima ba wai don ya ci mutuncin kowa bane.

CAN tace idan haka ne kowa ma yana fadin irin haka har shi gwamnan amma ba a tasa keyar kowa ba sai yanzu ace wai za abci wa wannan fasto mutunci, hakan ba zai sabu ba ko kadan sabo da haka gwamna El-Rufai ya shiga taitayin sa tun da wuri.

” Wannan gwamnati ta na muzguna wa kiristoci matuka saboda haka ba za mu zuba ido mu bari a ci gaba da yi mana bita kulle ba, ana yi mana zagon kasa ana ci mana mutunci ba . A barmu mu ji da azabar da ake ta gallaza wa kiristocin kasar nan haka nan da irin halin kakanikayi da aka saka mu.” Inji CAN.

Share.

game da Author