An samu gawar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda Gbolahan Olugbemi a mace a gidan sa.
Sai dai har yanzu babu tartibi ko takamaimen musabbabin mutuwar sa, amma dai mamacin wanda kafin mutuwar sa, ya na aiki ne a Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Legas, an sami gawar sa a rataye da igiya da aka ɗaure bisa bishiya, gawar na reto a cikin gidan sa, kusa da Jihar Oyo.
Wasu rahotanni dai sun ce ya kashe kan sa da kan sa ne, to amma dai ‘yan sanda ba su yarda cewa kashe kan sa ɗin ya yi ba.
An ji cewa mamacin wanda kafin mutuwar sa ya na aiki ne a Ɓangaren Binciken Manyan Laifuka (FCID), Alagbon a Legas, ya bar Legas ne da niyyar zai tafi Ogbomoso, Jihar Oyo domin yin hutun Easter a can.
An tsinci gawar sa na reto bisa bishiya wuyan sa ɗaure da igiyar da ke nuna alamun rataye kan sa ya yi, a ranar Litinin.
Duk da ana tunanin ko ya kashe kan sa ne, to dai bai bar wata wasiyyar da za ta iya tabbatar da hakan ba.
Mamacin ya taɓa zama ADC ns tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Alao Alaka, cikin 2006.
Kakakin FCID, Aminat Mayegun, ta tabbatar da mutuwar Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ɗin. Ta kuma ce ‘yan sanda sun fara bincike dangane da mutuwar sa.
Aminat ta ce mamacin wanda ya taɓa yi wa Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Israel Ajao AD, ba zai taɓa kashe kan sa da kan sa ba.
Discussion about this post