Asibiti a ƙasar Amurka ta sallami mutum na farko da aka dasa wa ƙodar Alade, bayan ya murnure sarai daga aikin tiyata da aka yi masa makonni biyu da suka wuce.
Rick Slayman yana murmurewa sosai kuma yanzu zai ci gaba da samum kulawa a gida tare da ƴan uwansa, kamar yadda babban asibitin Massachusetts da ke Boston ya sanar a kan X, tsohon Twitter.
Asibitin ya ce daga yanzu ma su fama da matsalar ƙoda sun warke, domin kosar Alade na zama daram a jikin mutum kuma ya yi aiki, sai da ana dan yi masa dabarbaru kafin a cire.
Likitoci sun ce sai an canja yanayin kwayoyin halittan aladen don ya yi daidai da tsarin halittar mutum ɗan Adam kuma ya yi aiki sumul kamar dama can na sa ne.
Discussion about this post