Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tsinci gawar wata budurwa mai shekaru 14, mai suna Shallon Ebitare a ban dakin wani otel dake Yenagoa.
Wannan lamari ya auku ne ranar Laraba yayin da mamaciyar da saurayinta mai suna Lucky Okubo mai shekara 17 suka kama ɗaki a wani Otel don shakatawa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Musa Muhammed wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce yarinyar ta mutu a cikin ban ɗakin Otel ɗin.
Muhammed ya ce an yi hanzarin kai ta asibitin FMC dake Yenagoa amma likita ya tabbatar cewa ta rasu.
Ya ce ‘yan sanda sun kama Okubo bisa zargin kisa sannan Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.
Zuwa yanzu Okubo na tsare a sashen SCID, Yenagoa yayin da ake ci gaba da bincike da nufin gano musabbabin mutuwar yarinyar.
Muhammed ya ce da zarar sun kammala binciken za su kai saurayin kotu domin yanke masa hukunci.
Discussion about this post