A cikin watanni shida da suka gabata akalla Falasdinawa 35,000 ne kasar Israila ta hallaka, daga cikinsu akwai kananan yara 15000. Amma sai satinda ya gabatane bayan sojojin Israila sun kai hari tareda hallaka mutum bakwai ma’aikatan World Central Kitchen sannan gidajen jaridun yammacin duniya suka farga da cewa kasar ta Israila ta zamo wata dodanniya wacce muradinta baya wuce zubarda jinin bayin Allah da basuji ba basu gani ba.
Akwai alamar tambaya anan
Shin ba jini bane ke kwarara a jijiyoyin larabawa da musulmi kamar yadda yake kwarara a jijiyoyin Nasara?
Shin jinin Turawa yafi jinin larabawa muhimmanci ne? Ko yafi shi ja ne?
Shin rayuwar Falasdinawa nada muhimmanci?
Shin rayuwa Amurkawa, Ingilawa da yan Ostireliya da Faransa tafi rayuwar Falasdinawa maza, mata da kananan yara ne?
Shin ta yaya duk wani mai hankali zaiyi nazarin irin wannan munafuncin karara?
Shin wannan ba wata mummunar wariyar launin fata bace?
Shin wannan ba wani mummunar mahangar mulkin mallaka bace wacce shuwagabannin turai suka samu Kansu a ciki ba? Hakan yasa basu kula da matsanancin halin rayuwarda Israila ke saka Falasdinawa a ciki ba?
Bayan shekaru 75 na mulkin mallaka, keta hakkin dan Adam da muke gani da idonmu a zirin Gaza wanda kadan ne daga cikin shuwagabannin kasashen yammacin duniya ke nuna kulawarsu, asali ma mafiyawancinsu sunyi kunnen uwar shegu da nuna halin ko in kula hadi da bada goyon baya ga irin wannan kisan kiyashin da kisan gilla hadi da wariyar launin fatan da duniya ta manta dashi tun lokacin mulkin wariyar launin fata na Nazi dayayi sanadiyyar yakin duniya na biyu.
Duba da irin wannan goyon baya da suke samu, shin abun mamaki ne yadda Yahudawa Zayonawa ke ganin Allah ya basu damar yin kisan kai da kisan kare dangi a inda sukeso da kuma lokacinda sukeso ?
Shin abun mamaki yadda kasar yahudawan ke ganin cewa zasu iya aikata ko wane irin zalunci ba tareda wani sakamako ko hukunci ba?
Shin abun mamaki ne yadda kasar ta Yahudawa Zayonawa ke ganin cewa sune kadai zababbin Allah kuma sunfi kowa?
Shin abun mamaki ne yadda suke ganin cewa su sunfi karfin duk wata doka duba da irin goyon baya da suke samu daga kungiyar NATO da sauran masu fada aji a yammacin duniya?
Watanni shida da suka gabata shuwagabannin yammacin duniya sun dage wajen bada goyon baya ido rufe ga kasar ta Israila data dage wajen kisan gilla akan Falasdinawa, mata da kananan yara dubbai ke mutuwa amma babu wanda ya daga murya sai da kasar ta Israila ta hallaka mutane bakwai turawa masu aikin jinkai a zirin na Gaza shine kasashen turai da Amurka dama yan kanzaginsu suka gane cewa lallai Israila ta haukace ta zama wata dodanniya daya kamata ayi maganinta.
Sufa wudannan shuwagabannin da sukayi kunnen uwar shegu lokacinda Israila ta hallaka Falasdinawa da ke kokarin karbar abinci daga motocin bada agaji da suka shigo daga kasar Masar.
A nasu gani yin hakan ba wani abun a kula bane ballantana ma a tsawata tunda wudanda aka kashe musulmai ne Larabawa.
Shin akwai adalci anan? Akwai wata kariya anan?
Shin wannan ba munafunci bane karara?
Shin wannan ba abun kunya da takaici bane ga wayewarmu ?
Shin Larabawa, yan Asiya, Bakaken fata ba mutane bane suma?
Haka watannin da suka gabata shuwagabannin yammacin duniya sun yi watsi da duk wani mai kira ko mai sharhi daya nuna masu cewa Firam Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya zamo mahaukacin kare da baya jin kiran uban gidansa.
Sun ki aminta da cewa Netanyahu ya zamo summun bukumun bayaji baya gani.
Sun ki aminta da cewa kisan kiyashinda Israila keyi a Gaza bawai addini bane kadai, wata mummunar akida ce ta Zayonawa, yan wariyar launin fata marasa imani da tausayi masu yunkurin shafe kasar Falasdinawa daga bayan kasa.
Maye da Netanyahu da yan anshin shatansa ke ciki yayi karfin da har Joe Biden wanda shine babban abokinsu kuma maitaimakonsu bai isa yayi magana su saurara ba.
Shin Zayonawa zasu taba yarda da cewa kisan mata, kananan yara, yan gudun hijira, yan jarida, likitoci, ma,aikatan majalisar dinkin duniya, da marasa lafiya da masu tabin hankali dama fararen hula da basuji ba basu gani ba da sunan Yahudawan duniya abune mai muni ba kuma wata barazana ce ga zaman lafiyar duniya ba?
Kamar yadda masu hikima ke cewa duk lokacinda kare ya haukace, ya ki jin maganar uban gidansa ya kuma yi yunkurin cizonsa to abunda yafi dacewa da wannan karen shine harsashi a tsakiyar kansa domin a fitardashi daga irin chakwakiyarda ya samu kansa a ciki.
Mai yiyuwa wannan itace mafita ga kasar Zayonawa.
Mai yiyuwa lokaci yayi da za,a kwantarda ita kamar mahaukacin kare a sheketa daga bayan kasa.
Na fada na kuma nanata duba da irin tabargazarda ta aikata watanni shida da suka gabata Israila bata da sauran wani yanci na wanzuwa.
Sannan kuma idan ambaton laifukan yaki da Israila ke aikatawa a Gaza da kuma kiran a tsagaita wuta zaisa a kakaba man lakabin kin jinin Yahudawa to muje zuwa.
Babu shakka wannan lakabin baje ne dazanyi alfaharin sakawa.
Ban aminta da kasar yahudawa ta ci gaba da karya dokokin kasa da kasa ba, ta kuma ci gaba da aikata laifukan yaki ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa to na aminta dashi.
Ban aminta da ake kashe ma,aikatan jinkai ba da yan jarida idan wannan shine kinjinin yahudawa to na aminta dashi.
Ban aminta da irin rashin imani da rashin ganin mutuncin dan Adam kamar yadda Bibi Netenyahu ya fito a gidan talabijin yana gayawa duniya yadda sojojinsa suka hallaka ma,aikatan jinkai 7 da basuji basu gani ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta dashi.
Ban kuma aminta da yadda kasar Israila ta kai hari a cibiyar jakadancin kasar Iran a birnin Damascus ba, ban kuma aminta da yadda kasar ta Israila ta hallaka sojojin Iran dake a cibiyar ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta dashi.
Ban kuma aminta da yadda kasar Israila ta kai hari a birnin Allepo dake kasar Syria ba inda ta kashe mutane 42 a ciki harda fararen hula ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta dashi.
Ban kuma aminta da cewa yahudawa nada lasisi daga Allah ba na kashe kananan yara idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta dashi.
Ban kuma aminta da cewa kasashen turai suci gaba da sayarwa kasar Israila da makamai ba suna masu taimakekeniya wajen kisan gilla da kisan kare dangi ga Falasdinawa. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma yadda da cewa yahudawa sune zababbin Allah ba ban kuma yadda da cewa sun fi sauran mutane ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa musulmai da kirista duka yan wuta bane ban kuma yadda da cewa Annabi Musulmai da Yesu kiristi duk jabun annabawa bane. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma yadda da cewa Yesu kiristi Sarki ne laifi ne ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma yadda da cewa Yesu kiristi mai ceto makaryaci bane, wai yana wutar jahannama yana konuwa cikin kashin bil,Adam ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa a rushe baitil mukaddis ba, kana a yanka shanu jajaye guda uku a wajen kafin a gina majami,ar yahudawa ta uku a wajen daidai ne ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da irin yadda yahudawa suka mamaye madafan ikon kasar Amurka ba, da kuma siyasar duniya da bankunan duniya da kuma manyan gidajen jaridun duniya ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa domin an kaiwa kasar Israila hari tanada yancin ta kashe duk wani Bafalasdine kota kora Falasdinawa zuwa cikin Sahara ko kuma ta watsasu dukansu cikin teku mata, da maza yara da manya. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa wai Zayonanci daga Allah bane, zayonanci wata mummunar akidace tafi akidar Nazin Hitla muni. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa a kori Candace Owen daga Daily Wire ba saboda ya soki lamirin Israila ba ban kuma aminta da cewa Rabbi Shmuly da Ben Shapiro mutane ne ba. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa Bibi Netanyahu nada hankali ba, ban kuma aminta da cewa abunda yakeyi yana kare muradin Yahudawa bane ko kasar Israila. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa Afrika ta Kudu da kuma kasar Ireland sun aikata wani kaifi ba don sun shigarda karar Israila zuwa kotun kasa da kasa ta ICJ ba akan laifukan yaki, kisan kiyashi da kuma mulkin mallaka. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa Israila nada yanci hana shigar kayan abinci zuwa zirin Gaza ba a lokacinda mata da kananan yara ke mutuwa saboda yunwa. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa duk kasashen musulmai su hada kai su fuskanci Israila ba, abunda na aminta dashi shine duk kasashen duniya kona musulmai ko kirista ko Hindu su hadakai su fuskanci Israila. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Ban kuma aminta da cewa kisan gilla, kisan kare dangi da kuma shafe wata al,umma daga bayan kasa itace mafita ga rashin jituwar kasa da kasa ba. Ina matukar yin Allah wadai da kisan kiyashinda akeyiwa mutanen Gaza. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Daga karshe na dawo daga aminta da cewa kasar Israila nada yanci cigaba da wanzuwa ba. Na aminta da cewa sun wofantarda yancinsu na wanzuwa a daidai lokacinta suka zabi su sha jinin matan Falasdinawa suyi wanka da jinin yara Falasdinawa su kuma yi masu kisan gilla. Idan wannan shine kin jinin yahudawa na aminta da shi.
Shekaru 75 da suka gabata Allah cikin ikonsa ya bawa Yahudawa sabon matsuguni da zimmar dawo masu da karamcinsu.
Wannan baiwace mai matukar muhimmanci amma sun wofantarda ita ta hanyar yiwa Falasdinawa Nakba, suka ki aminta dasu raba kasar tsakaninsu da Larabawa wudanda suka samu a wajen. Suka koma yan mulkin mallaka suna azabtardasu kamar dabbobi suna sace filayensu da dukiyoyinsu cikin izgianci.
Abun bakin ciki sunyi amfani da hannunsu sun wofantarda baiwar da Allah yayi masu. Suna aikata irin rashin imanin da Nazi suka taba aikatawa a kansu.
Idan za,a fadi gaskiya sam Israila ba demokradiyya bace, kasace ta yan handama da babakere, masu kishin zubarda jini, dodanni yan mulkin mallaka da mulkin wariyar launin fata tsakanin yahudawan turai da kuma Falasdinawa Larabawa da sauran su.
Kazancewa balarabe ko kirista Israila ba karamin kunci bane, domin hakan na nufin a ko wane lokaci zaka iya shiga halin kisan gilla, kisan wariyar launin fata ko kisan kiyashi daga kasar yahudawa a duk lokacinda suka so kuma sukaga dama.
Akan wannan dalilin ne kasashen duniya suke fushi da kasar ta Israila, haka kuma duk wani mutum mai nazari, hankali, tunani da imani a zuciyarsa.
Gaba dayansu suna fadar DAGA RAFI ZUWA TEKU FALASDIN ZATA SAMU YANCI.
Kuma duk da munafuncin shuwagabannin yammacin duniya hakan zaikasance cikin sunan Allah rayayye.
Femi Fani Kayode, Sadaukin Shinkafi.
Discussion about this post