Akilu Abdullahi ya kan ziyarci mahaifiyarsa a kullum da safe kafin ya tafi wurin aiki. Sai dai kuma Allah bai bashi ikon yin haka ba ranar 2 ga Janairu.
Daɗaɗɗiyar burin Abdullahi shine ya zama Limamin masallaci, sai dai kash, wannan buri tasa bai tabbata ba domin a wannan rana yana hanyar zuwa kasuwa sojoji suka kama shi suka tafi da shi. Tun daga wannan rana bai dawo gida ba shi kenan sai a lahira.
Mahaifiyar sa da ‘yan uwansa ba su sake ganin sa ba sai dai hoton sa a waya kwance a daji mace da shaidar ramukan ratsawar harsasai a koina a jikinsa.
Ko a lokacin da PREMIUM TIMES ke tattaunawa da mahaifiyar sa, hawaye ba su daina ruba daga idanunta ba.
Kwanaki uku gabanin bacewar Abdullahi, Nura Yusuf ya tafi kasuwar mararraba ta Katul da ke karamar hukumar Kachia a Kaduna a ranar Asabar 30 ga watan Disamba domin sayar da akuya da buhun hatsi. Jim kadan da isa kasuwar sai wani mutum da ke sanye da kakin sojojin Najeriya ya harbe shi har lahira.
A cewar wani da abin ya auku a idonsa, an harbi Yusuf ne a kirji nan take sannan sojojin suka rika harbi sama suna Ihu. Daga nan sai suka jefa gawar Yusuf da babur dinsa cikin motar sojoji suka tafi. Daga baya an tsinci gawarsa an jefar da ita a kusa Oduma, wani kauye a Kachia.
Wadannan sune irin bala’in da suka rika faruwa tsakanin wannan lokaci a kauyen Tilde Fulbe wanda mutane ke ganin yadda ake kashe ‘yan uwansu babu gaira babu dalili, suna cikin tsananin tsoron kada irin haka suma ya afka musu, ganin makwabta suke da wannan kauyen.
Tun daga 21 ga watan Disamba zuwa 10 ga watan Janairu, sojoji, dare da rana, sun rika afkawa Tilde Fulbe, suna kame, kwace da kuma kashe mutanen da ba su ji ba basu gani ba.
A bincike da PREMIUM TIMES ta yi na tsawon wata guda, ta gano yadda Sojoji suka rika cin karen su ba babbaka a wanan gari suna shiga suna kwace, kisa, sata kamar yadda mutanen garin suka shaida wa jaridar sannan kuma da binciken mai zurfi da ta yi ta bankaɗo ta’asar da sojoji suka tafka a wannan kauye.
Al’ummar garin Tilde Fulbe sun bayyana sunayen wadanda sojoji suka kashe kamar haka, Akilu Abdullahi, Ibrahim Abubakar, Safiyanu Adamu, Abdulaziz Yusuf, Magaji Umar, Abdulkadir Idris, Saidu Saleh, Nura Magaji, Ibrahim Sani, Musa Dan Asabe, da Nura Yusuf.
Sai dai kuma rundunar sojin Najeriya ta musanta aikata wani abu da ya saba wa doka a aikin tsaro da ta yi a wannan yanki a lokacin.
Sojoji sun ce sun sami labarin ‘yan ta’adda a wannan yanki suna addabar mutane, kuma wannan ne dalilin da ya sa suka kai farmaki amma ba gaskiya bane wai sun kashe mutane haka kawai.
PREMIUM TIMES ta gano cewa duk da tsananin rashin tsaro da ake fama da shi a jihar Kaduna musamman a wannan yanki na kudancin Kaduna, ba a taba samun labarin ta’addanci na kowani iri daga wannan yankin na Tilde Fulbe.
“Sojojin Najeriya ba za su taba aikata irin wannan danyen aikin ba,” kakakin rundunar Nwachukwu ya shaida wa PREMIUM TIMES. “Wadannan zarge-zargen galibi ana kawo su ne a duk lokacin da sojojin Najeriya ke samun nasara a yakin da suke yi da ta’addanci.”
Haka shima Yahaya, jami’in yada labarai na rundunar a Kaduna, ya tabbatar cewa “babu wani lokaci da sojoji na rundunar suka kashe wani Bafulatani makiyayi ko wani ko wani wanda ba mai laifi ba kuma wai har suka kwace masa babur da buhun Cittar sa. Duk zuki tamalli ne kamar yadda ya bayyana mana.
Sai dai kuma wasu daga cikin iyalan wasu daga cikin wadanda aka kashe, sun bayyana cewa lallai jami’an sojoji sun zo har kauyen sun roƙe mutane yafiya, kuma sun yi musu alkawarin za su gudanar da bincike akai.
Discussion about this post