Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi tir da garkuwa da ɗaliban sakandare 287 a garin Kurebe, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.
Haka nan kuma ya jajanta dangane da arcewa da ‘yan ta’adda suka yi da matan karkara har ƙimanin 200, a Gamboru Ngala, cikin Jihar Barno.
Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaban , Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya bayyana sace mutanen kusan 500 a rana da cewa babban laifi ne sosai a kama marasa galihu a yi garkuwa da su.
Daga nan Tinubu ya umarci jami’an tsaro da jami’an leƙen asiri cewa su gaggauta ceto waɗanda aka yi garkuwar da su, kuma a tabbatar an kamo tare da hukunta waɗanda suka yi garkuwa da su.
PREMIUM TIMES ta ga rahotannin da suka tabbatar da cewa ɗalibi ɗaya da ‘yan ta’adda suka harba a Kurebe, ya rasu bayan ya kwana asibitin da aka garzaya da shi.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda ‘yan ta’adda suka arce da ɗalibai 287 a Kaduna, mata 200 a Barno, sa’o’i 48 bayan Ministan Tsaro ya yi shelar matsalar rashin isassun sojoji.
Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla ɗalibai ‘yan firamare da na sakandare 287 ne ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuriga, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, a safiyar Alhamis.
Gidan Radiyon BBC ya ruwaito cewa wani malamin makaranta mai suna Sani Abdullahi, ya bayyana yadda ya kuɓuta, kuma ya tabbatar da cewa ɗalibai 287 ne aka sace a safiyar.
“A ɓangaren sakandare ɗalibai 187 suka ɓace, a ɓangaren firamare kuma ɗalibai 125 ne da farko ba a gani ba. Amma daga bisani guda 25 sun dawo.”
Malamin ya bayyana haka a lokacin da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya ziyarci makarantar, domin gani da ido kan yadda lamarin ya ke.
Ya ce, “na shigo makaranta misalin ƙarfe 7:45 na safe, sai na shiga ofishin shugaban makaranta ɓangaren sakandare. Kawai sai ya ce min in waiga baya. Ina juyawa sai na ga ‘yan bindiga sun kewaye makarantar.
“Mun ruɗe ba mu san inda za mu ba. Kafin su shiga da mu daji sai muka canja hanya,” inji Sani Abdullahi.
Ya ce mahara sun kashe mutum ɗaya, sauran yaran da aka gudu da su ɗin shekarun su sun kama ne daga 28 zuwa 15.
Wani kuma ya ce babu gidan da wannan lamari bai shafa ba a Kuriga.
Discussion about this post