Jam’iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shugabar mata na jam’iyyar saboda ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai.
Idan ba a manta ba, tun bayan caccakar gwamnatin El-Rufai da magajin sa Uba Sani ya yi masoya da magiya bayan jigajigan biyu suka shata layi a tsakanin su a jihar.
Uba Sani ya bayyana a wajen taro a Kaduna ranar Asabar cewa El-Rufai ya tattago basuka lokacin da yake gwamnan Kaduna da yanzu tarin bashin ya sa ko albashi ba ra iya biya.
Sai dai kuma shugaban mata ana APC Maryam Suleiman, da aka fi sani da MaiRusau ta maida wa gwamnan da martani inda ta ce masa kuka bayan hari ya ke yi.
” Kuka bayan hari kake yi gwamna, za ka ce ba ka san da bashin bane lokacin da kake neman gwamnan ido rufe. Ka hana kowa zama kai ne can kai ne nan sai ka zama gwamna.
” Yanzu ka zama kuma ya na neman dora wa tsohon gwamna laifi. Ai da baka nemi kujerar gwamnan ba.
” Tunda ka ce ba kuɗin da za ka yi aiki sai ka tarkata ka kara gaba, ka yi murabus kawai. Kuma ai da kai aka ciyo bashin kana kan gaba wajen ciyo bashin kuma yanzu ka zo ka ce wai ai babu kuɗi.
Bisa waɗannan kalamai ne Jam’iyyar ta dakatar da ita ta ce za ta gudanar da bincike akai.
Jam’iyyar ta ce akwai hanyoyi da dama da yakamata Maryam tabi a jam’iyyarce domin warware irin matsala kamar yadda dokar jam’iyyar ta gindaya, ba kawai a hau shafikan sada zumunta ba a riga surutai.
Discussion about this post