Daɗaɗɗiyar matsalar wutar lantarki a kullum sai ƙara ƙamari ta ke yi, ta yadda tun ana cewa matsalar ta ɓaci, har aka kai ana cewa ta yi muni, har ga shi daga ƙarshen shekarar da ta gabata zuwa yanzu matsalar ta tashi daga muni, ta ma ƙazanta baki ɗaya a faɗin ƙasar nan.
Saboda tun ana yawan ɗauke wuta a sassa daban-daban, sai an ɗauki lokaci a maido, har ta kai ƙazantar matsalar ta kai baki ɗayan ƙasar na afkawa cikin dubu – durunɗum.
A kowace rana a ɓangaren shugabanni na sama na zargin na ƙasa da laifin matsalar, kamar yadda su ma na ƙasan ke ɗora laifin matsalar a kan na sama.
Matsalar wutar lantarki ta durƙusar da manya, matsakaita da ƙananan masana’antu da sana’o’i daban-daban. Haka samun rangwame wajen gudanar da rayuwa cikin sa’ida ya zama alaƙaƙai, a gefe ɗaya magidanta na fama da gaganiyar tsadar fetur da gas, wanda za su yi amfani wajen tayar da janareto a gidajen su. Janareto kaɗai sai ya ƙaras da kuɗin aljihun magidanci ƙarƙaf. Yanzu barci mai daɗi kuma mai nauyi ba shi yiwuwa a gidaje, raboda tsananin rashin wutar lantarki. Wannan kuwa babbar matsala ce ga lafiyar jama’a!
Baya ga durƙushewar tattalin arziki da haifar da rashin aikin yi, matsalar wutar lantarki ta na ƙara ruruta matsalar tsaro a faɗin ƙasar nan. Saboda fashi da sauran manya da ƙananan laifuka sai ƙara ta’azzara suke yi a cikin duhu.
Kamfanonin bada wutar lantarki wato DisCos da Kamfanin Samar da Wuta wato TCN su na danganta matsalar wutar da ake fama da ita a yanzu da matsalar rashin wadataccen man gas da ake tura wa Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki wato GenCos.
A Ibadan da sassan Jihar Ogun da wasu sassa, ana danganta matsalar da yawan sace kayan wutar lantarki mallakar TCN da kuma satar wutar da ake yawan yi.
Ko cikin makon jiya a wurin taron da Ministan Makamashi ya yi da masu ruwa da tsaki kan harkokin wutar lantarki, ya zargi DisCos da ƙin karɓar gejin ƙarfin wutar da aka rarraba masu. Wanda hakan ya haifar da jefa ƙasar nan cikin duhu – durumɗum. Ministan a cikin fushi ya nuna rashin cancantar wasu DisCos ɗin a harkokin hada-hadar makamashi.
A kan haka ne ministan ya gargaɗe su cewa su ƙara maida himma wajen ƙara isa da wutar lantarki ko kuma ya soke lasisin su.
Ita kuma Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki (NERC) an ce ta tsaya a cikin shiri a wannan yanayi da ake ciki.
A duk duniya babu wata ƙasar da za ta riƙa sakaci da wutar lantarki kamar yadda Najeriya ke yi, kuma ta yi tunanin samun nasarar tattalin arziki.
Lokacin da aka rushe PHCN cikin 2013 aka kasa ta gida 11, an yi tunanin yin hakan zai warware matsalar lantarki a ƙasar nan. Sai dai abin takaicin hakan sai ma ƙara dagula matsalar ya yi sosai.
Lalacewar lamarin ya kai yanzu a ƙasar nan ƙarfin wutar da ake samu ba ta wuce daga migawats 3000 zuwa 4,500 ba, duk kuwa da ɗaukin Naira tiriliyan 1.6 maƙudan kuɗaɗen da CBN ya bayar domin inganta wutar lantarki, lamarin da wasu masana suka ce dusa ce kawai aka shuka a idon makwarwa, domin harkar wuta ai ta ‘yan kasuwa ce.
Akwai harƙalla da cuwa-cuwa a kamfanonin DisCos sosai, yadda ba su so su riƙa bayar da mita, sun fi so su riƙa bayar da wuta kai-tsaye su caji masu biyan kuɗi ba da tare da ɗaura masu mita.
Akwai a cikin shekarun baya ma lokacin da wani mai kamfanin DisCos ya ce a matsayin su na ‘yan kasuwa, tilas sai mun riƙa sanin inda muka dosa, tare da nazarin shin tsarin mitar ita kan ta, shin zai iya kai mu ga inda muke so mu mu ga mun kai ɗin kuwa? To idan muka ga tsarin raba mita ba zai kai mu ba, sai mu yi watsi da ita.” Wannan kuwa ya saɓa wa tsarin da duk duniya ake a kan sa.
Wannan gidoga ce ta sa aka gano cewa daga cikin kwastomomin wutar lantarki miliyan 12.8 a Najeriya, guda miliyan 5.7 ne kaɗai ke da mita, a ƙididdgar watan Fabrairu, 2024.
Akwai ruɗani dangane da maƙudan kuɗaɗen da DisCos ke bin Fadar Shugaban Ƙasa da wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya guda 86, saboda akwai aringizo a kuɗaɗen, kasancewa yawanci ba da mita aka yi amfani wajen tantance adadin yawan kuɗaɗen.
Gwamnatoci uku da suka shuɗe, wato ta Goodluck Jonathan, ta Muhammadu Buhari duk su na cikin wannan tarangahuma, har yanzu ta zo kan gwamnatin Bola Tinubu.
A duk duniya sai komai komawa ya ke yi a hannun ‘yan kasuwa, domin a samu ci gaban tattalin arzikin ƙasa. Amma a Najeriya, sai ma ƙara lalacewa lamarin ya ke yi.
Yanzu dai lokacin sake bibiyar yarjejeniyar kwangilolin sayar da wutar lantarki ga DisCos a Najeriya ya yi su da GenCos. Idan ba su iya kai aƙalla gejin da ake buƙata wajen samar da wutar lantarki, to a gaggauta soke kwangilar.
Saboda tattalin arzikin Najeriya da su kan su ‘yan Najeriya su na buƙatar wutar lantarki domin su ci gaba da rayuwa. Saboda harkokin tafiyar da rayuwar yau da kullum fa sai da wutar lantarki.
Discussion about this post