Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta samar da wata hanya domin dakile yaduwar zazzabin Lassa musamman a jihohin da ke fama da barkewar cutar duk shekara.
Ministan muhalli Iziaq Salako ya sanar da haka a farkon wannan mako a Abuja a taron da ya yi da manema labarai kan yaɗuwar cutar a asibitin sojoji na 44 dake Kaduna.
Salako ya ce gwamnati za ta kafa kwamiti wanda za kirkiro hanyoyin da za a gama da ɓeraye da su ne ke saka wannan cuta.
Salako wanda babban sakataren ma’aikatar muhalli Ibrahim Idris ya wakilta a wurin taron ya ce kwamitin da gwamnati za ta kafa za ta tattauna da jami’an lafiya na jihar Kaduna domin tsara hanyoyin da za a bi don yakar cutar.
Masu gudanar da bincike kan cututtuka na jihar Kaduna sun bayyana cewa zuwa ranar 25 ga Fabrairu daga cikin mutum 12 din da aka yi wa gwajin cutar 6 sun kamu yayin da mutum biyar sun mutu.
“Akwai wasu mutum biyu daga asibitin Barau Dikko da ake zargin sun kamu da cutar. An killace mutum 92 bayan an tabbatar sun yi cudanya da wadanda suka kamu da cutar.
Matakan yakar cutar da gwamnati ta dauka
1. Saka maganin beraye a asibitocin jihar Kaduna domin gama wa da su.
2. Kafa duba garin da za su rika sa idon gano unguwanni, garuruwa da beraye ke damun su domin a gama da su.
3. Hada hannu da masu wuraren siyar da abinci, wuraren shakatawa, otel, kasuwanni da tashoshin mota domin kawar da beraye.
Salako ya ce hukumar EHCON za ta bada satifiket din kawar da beraye ga duk wuraren da suka yi nasarar fatattakar berayen da suka addabe su.
Rajistarar hukumar EHCON Yakubu Baba ya ce bana hukumar za ta maida hankali wajen wayar da kan mutane tare da daukan matakai domin yakar cutar.
Discussion about this post