Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana halin da ake ciki a Najeriya cewa wasu gungun masu neman durƙusar da ƙasar nan ne ke mata maƙarƙashiya da zagon-ƙasa.
Shettima ya ce wasu da ba su samu nasarar lashe zaɓe da yawan ƙuri’u na ke ta ƙoƙarin yi wa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu zagon-ƙasa da maƙarƙashiya.
Mataikakin Shugaban Ƙasa ya bayyana haka a ranar Talata, inda ya ce wasu da ba su ci zaɓe ba ne ke ta maƙarƙashiya ga gwamnatin TInubu da kuma wasu ‘yan sumogal.
Ya furta hakan ne lokacin da ya ke jawabi wurin Taron Dabarun Tattalin Dukiya, wanda aka yi a Abuja, a ranar Talata.
“Gungun wasu ƙarfafan da ba su ci zaɓe ba ne ke neman jefa ƙasar nan cikin ruɗani, ina nufin waɗanda ba su samu mulki yawan ƙuri’u ba. Maimakon su jira sai nan da 2027 sannan su sake jaraba sava, sai idon su ya rufe, suke ganin gara ma ƙasar ta durƙushe, kowa ma ya rasa, babu abin da ya dame su. Amma za su kai masu damƙa,” inji Shettima.
“Cikin ‘yan kwanakin nan an kama tirela 45 da lodin masara za a fita da su maƙauciyar ƙasar mu.
“Kuma a can dai kan iyakar Illela ɗin a Jihar Sokoto, akwai ɓarauniyar hanyar fita da shigo da kaya har guda 32. Yanzu farashin buhun masara ya sauka daga Naira 60,000 zuwa 50,000.
Discussion about this post