Binciken da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya gudanar, ya nuna cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kasa yin bayanin yadda aka yi da wata Dala biliyan 4.5 da aka kamfata daga Asusun Kuɗaɗen Wajen tsakanin 2018 da 2019.
Rahoton shekara-shekara na Ofishin Akanta Janar ɗin kan yadda ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya suka kashe kuɗaɗen su, ya nuna cewa an rasa yadda CBN ya yi da kuɗaɗen, kuma babu su, babu dalilin su.
Salwantar kuɗaɗen dai ta faru ne lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, a ƙarƙashin tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, wanda a yanzu haka ke tsare ya na fuskantar tuhuma.
Rahoton ya ce adadin kuɗaɗe ne ajiye har Dala 42,594,842,852.75 a cikin 2018. Amma abin mamaki, cikin Disamba, 2019 sai kuɗaɗen suka koma Dala 38,092,720,200.00.
Wato a ƙididdige an kafci Dala biliyan 4,502,122,652.03 kenan, kuma an rasa yadda aka yi da kuɗaɗen.
Daga nan Akanta Janar ta Tarayya, Shaakaa Chira, ta nemi CBN ya fito da sahihan bayanai, ko kuma a fito da kuɗaɗen.
Kuma ta yi gargaɗin cewa maganar da CBN ke yi na ƙoƙarin saisaita akalar Naira a kasuwar musayar kuɗaɗe na cikin hatsari babba.
Discussion about this post