Yayin da ake cikin mummunan mawuyacin halin tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci da na sauran kayan masarufi, wani sabon rahoton da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ya fitar, ya nuna yadda malejin tsadar rayuwa ya yi saɓulewar da tuni talakawa suka fara saduda daga neman mafiya.
Ma’aunin tsadar rayuwa ta tashi daga kashi 28.92 a ƙarshen Disamba, 2023, inda yanzu ya dangwali malejin kashi 29.90 a ƙarshen Janairu 2024.
Wannan lamari na faruwa ne daidai lokacin da talakawa suka fara fita zanga-zangar neman sauƙin rayuwa a jihohin Neja, Kano da Sakkwato.
A Jihar Kano kuma tuni Hukumar Hana Cin Rashawa da Amsar Ƙorafe-ƙorafe ta fara bi cikin kasuwanni ta na fasa kantinan da aka ɓoye abinci, da nufin sai ya ƙara tsada a sayar.
Alƙawarin kawo mafitar da gwamnatin tarayya ta yi mako biyu da ya gabata, shiru ka ke ji, in banda kwamitin da aka ce an kafa.
Har yau ba a ji ba daga gwamnatin tarayya tun bayan da ta ce za ta fito da abinci daga rumbunan ajiyar abincin ta, domin rabawa jihohi don a samu sauƙin rayuwa da sauƙin farashi.
Wani sabon rahoto bayyana kayan abincin da ya gagari talakawa a halin yanzu.
Tuni a wasu garuruwa sukari ya gagari talaka, an koma amfani da mazanƙwaila.
Gidaje da yawa inda a baya yara ba su san garin kwaki ba, a yanzu shi ne abincin su a ranar da suka samu.
Ana cikin wannan mamuyacin halin ne kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta cire tallafin fetur, domin tattalin na wannan shekara ta 2024 ya kai naira tirilan 2.9, amma Naira miliyan 450 kawai gwamnati za ta iya biya a ɓangaren tallafin.
Umarnin A Tsaida Farashin Abinci Daga Kotu:
A farkon wannan wata ne dai kotu ta umarci Gwamnatin Najeriya ta tsaida farashin fetur, abinci da kayan masarufi.
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta umarci Gwamnatin Tarayya ta tsayar wa fetur takamaimen farashi, haka sauran nau’o’in kayan abinci da kayan masarufi.
Kotun ta umarci Gwamnatin Bola Tinubu ta tsaida farashin kayayyakin cikin kwanaki bakwai daga ranar Laraba, ranar da ta bada umarnin.
Musamman kotun ta nemi gwamnati ta tsaida yankakken farashin sukari, madara, filawa, gishiri, keke da kayan gyaran sa, babura da kayan gyaran su, motoci da kayan gyaran su da kuma fetur, gas da dangogin su, ciki har da kananzir.
Mai Shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ne ya yanke wannan hukunci, bayan ya saurari ƙarar da fitaccen lauya Femi Falana 6a shigar.
Mai Shari’a ya ce lauyoyin Gwamnatin Tarayya ba su yi jayayya da wannan hukuncin da aka yanke ba.
“Saboda dukkan roƙon da mai shigar da ƙara ya nemi kotu ta yi masa, an amince”, inji kotu.
Sai dai kuma wannan hukunci bai bayyana irin hanyoyin da gwamnati za ta bi domin tsaida farashin kayayyakin ba, musamman waɗanda aka lissafa.
Ba a dai sani ba ko wannan umarnin ya shafi har umartar gwamnatin tarayya ta soke cire tallafin fetur, wanda ta yi tun farkon hawa mulkin Shugaba Bola Tinubu.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin da gwamnatin tarayya ta ce ta damu dangane na tsadar kayan abinci da ake fama, lamarin da ta kai har wasu mata suka fito suka yi zanga-zanga a Minna, babban birnin Jihar Neja.
A labarin an nuna cewa zanga-zangar mata a Minna ta razana Gwamnatin Tarayya, Shugaba Tinubu ya bada umarnin sasauta farashin kayan abinci.
Zanga-zangar da mata suka gudanar a Minnna, babban birnin Jihar Neja dangane da tsadar kayan abinci da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya, ta razana Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, lamarin da ya ƙara zaburar da shugaban bada umarni ga hukumomin da abin ya shafa su gaggauta daƙile hauhawar farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ne ya bayyana haka, bayan tashi daga taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Raba Agajin Abincin Gaggawa ya yi ranar Talata, a Abuja.
Idris ya ce Shugaban Ƙasa ya damu sosai dangane da yadda abinci ke ƙara tsadar nesanta kan sa daga talakawa a faɗin ƙasar nan.
“Gwamnati ta damu ƙwarai dangane da halin da ‘yan Najeriya ce fama yanzu, musamman abin da ya faru a Minna jiya Litinin,” cewar ministan, yayin da ya ke buga misali da zanga-zangar da mata suka fito a Minna, dangane da tsadar abinci.
“Kan haka ne gwamnati ta fara ɗaukar wasu matakai domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu sauƙi da rahusa, ta yadda abinci ba zai riƙa neman gagarar su ba.”
Ministan ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da yin taro har zuwa ranar Alhamis. Ya ce tuni har an fara ɗaukar wasu muhimman matakai, domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci.
“Daga cikin matakan akwai gaggauta fito da kayan abincin da gwamnatin tarayya ta tanadar a Rumbunan Ajiyar Abincin Gwamnati da ke faɗin ƙasar nan.
“Sannan kuma gwamnati na tattaunawa da manyan masu sarrafawa ko cashe kayan abinci da manyan ‘yan kasuwar kayan abinci da kayan masarufi, domin tantance adadin abin da suke da shi ajiye a runbunan ajiyar su.
“Dalilin yin hakan shi ne gwamnati na so ta gaggauta shiga cikin lamarin, domin abinci ya wadata ga ‘yan Najeriya.”
Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa gwamnati na sane akwai wasu wasu marasa kishi kuma marasa tausayi da ke ɓoye abinci domin su sayar idan ya yi tsada sosai.
“Abin da zan shaida wa ‘yan Najeriya shi ne, Shugaban Ƙasa ya bada umarni cewa gwamnati ta gaggauta shiga cikin wannan lamari domin kawo sauƙi, ta hanyar daƙile masu ɓoye kayan abinci.
“Gwamnati ba za ta zura ido ‘yan Najeriya na fama da tsadar kayan abinci ba, alhali wasu na haifar da ƙarancin sa. Don haka ina roƙon jama’a su fahimci irin damuwar gwamnati da kuma ƙoƙarin da ta ke yi.
“Yayin da aka kammala waɗannan tarukan, za mu fito da sanarwa dangane da matsayi da matakan da gwamnati ta ɗauka.” Inji Idris.
Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Yemi Cardoso, Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun da Mashawarcin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Ministan Noma, Abubakar Kyari, na Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, sai kuma Ƙananan Ministocin Gona da FCT Abuja, Sabi Abdullahi da Mariya Mahmood.
Discussion about this post