Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta koka da yadda cutar bakon dauro ke yaduwar a duniya gaba daya inda kungiyar ke cewa an samu karin kashi 79% na yaduwar cutar a shekarar 2022.
Mashawarciya kan aiyukka na yakan cututtukan bakon dauro da Rubella (German measles) Natasha Crowcroft ta bayyana cewa an samu karuwa a yaduwar da yawan mutanen da cutar ke kashewa a dalilin rashin maida hankali wajen yin allurar rigakafi.
Natasha ta ce yaduwar cutar na tada hankalin jami’an lafiya musamman yadda ba duk wuraren da cutar ke bulla ake sani ba.
Ta ce ana hasashen cewa cutar ka iya bulla a sama da rabin kasashen duniya nan da karshen wannan shekara sannan ana zaton cewa yara miliyan 142 ne za su kamu da cutar a wadannan kasashe.
“A shekarar 2022 an samu Karin kashi 43% a yawan yaran da cutar ta kashe inda bisa ga yadda cutar ke yaduwar za a samu karin yawan yaran da za su mutu a dalilin kamuwa da cutar a 2023.
Natasha ta ce kamata ya yi a samu akalla kashi 95% na yaran da aka yi wa rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar amma zuwa yanzu yara kashi 83% ne suka yi rigakafin cutar.
Ta ce kashi 92% na yaran da suka fi kamuwa da cutar na zama ne a kasashe ma su tasowa.
Cutar ta bulla a Amurka, Burtaniya da Ireland
Discussion about this post