Mushin Ibrahim, ɗan shekara 14, ya rasa ransa a lokacin da wata motar bas kirar J5 Peugeot da jami’an hukumar kwastam ta biyo a Jibia ta afkawa jama’a a ranar Asabar.
Shaidu sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa, jami’an hukumar kwastam sun biyo motar bas din ne a lokacin da ta murkushe yaron da misalin karfe 11 na safe a garin Jibia.
Hadarin ya afku ne a kusa da makarantar firamare ta Tudun Wada, Tashar Huraira a cikin garin Jibia.
” Muna zaune a kofar gidan mai na Masara ne hatsarin ya afku. Direban J5 din dai yana cikin tsananin gudu yana kokarin tsere wa daga hannun jami’an kwastam sai ya rasa yadda zai yi da sitiyarin motar sai ya ci karo da jama’a amma yaron ne kawai ya murkushe” wani ganau da ya bayyana sunansa da Buhari ya shaida wa PREMIUM TIMES. “Mu ma mun yi sa’a. Wasu kuma sun yi sa’ar tserewa.”
Ya ce motar kwastam din ta juya ta koma shingen bincikensu bayan hatsarin.
Duk da cewa an rufe iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata, masu fasa-kwauri na ci gaba da shigo da kayayyaki da aka haramta.
Shugaban kungiyar Jibia Peoples Forum, Gide Dahiru, ya ce direban J5 ɗin ya sanar da su cewa waken soya ce ya siyo a daga Batsari ba jamhuriyar Nijar ba.
Discussion about this post