Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙaryata raɗe-raɗi, zargi da wata kafar yaɗa labarai ta fitar cewa zai canja Dala biliyan 30 da ke ajiye a bankin zuwa naira.
CIkin wata sanarwa da Daraktan Riƙo na Yaɗa Labaran CBN, Hakama Ali ta fitar a ranar Asabar, ta ce zargin ba gaskiya ba ne, wasu ne dai kawai ke naman tada hankalin jama’a domin cusa tsoro a kasuwar hada-hadar musayar kuɗaɗe.
CBN ya nuna damuwa dangane da yadda ake ta ƙirƙirar ƙarya da karkatattun bayanai ana dangantawa ko alaƙantawa da bankin, don kawai a kawo cikas wajen ƙoƙarin da CBN ke yi domin ya saisaita tattalin arzikin Najeriya.
“Irin wannan ƙarairayin fa an yi su ko masu kama da su a watannin baya. Wato dai kenan akwai wasu ‘yan ƙaƙuduba masu ƙoƙarin ganin yi wa CBN zagon-ƙasa.
“Mu na son tabbatar wa jama’a cewa CBN na aiki haiƙan domin kawar da duk wani shakku, kuma ba zai taɓa yin duk wani tsarin da zai kawo wa kuɗin Najeriya da tattalin arzikin ƙasa zagon-ƙasa ba.” Cewar ta.
Discussion about this post