Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa jami’an ta sun tsinci gawar wani mutum mai suna Nuruddeen Shehu bayan ya rataye kansa a unguwar Gadon Kaya da ke karamar hukumar Gwale a cikin birnin Kano.
Shehu da ke aikin gadi a makarantar firamaren Prestige Academy dake layin Damisa a unguwar Gadon Kaya ya yanke hukuncin kashe kansa ne ta hanyar rataya bayan ya samu labarin tsohuwar matarsa ta yi aure.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Usaini Gumel ya ce jami’an rundunar sun tsinci gawar mamacin sakale a ɗaya daga cikin ajujuwan makarantan.
“A ranar 28 ga Janairu da misalin karfe 10:30 na safe wani Abdullahi Abdulsalam dake zama a unguwar Rijiyar Zaki ya sanar da ‘yan sanda abin da ya faru.
Gumel ya ce tuni ‘yan sanda suka dauki gawar zuwa babban asibitin Murtala Muhammed inda likita ya tabbatar ya mutu.
Ya ce tuni an fara gudanar da bincie domin sanin ainihin musabbabin mutuwar sa
Jihar Kano na samun karuwa a yawan mutanen da ke kashe kansu domin ko a cikin kwanakin bayan an samu irin haka na wani mutum a unguwar Sauna kawaji da kuma garin Tsamiya de ke karamar hukumar Gezawa, duk sun kashe kansu.
Discussion about this post